Shin, Wai Da Gaske Mahaifan Annabi (S.A.W.W) Na Wuta??? (2)




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YANA DAGA CIKIN HADISAN QARYA DA AKA QIRQIRO DON CIN ZARAFINSA (S.A.W.W )

Cigaba :-

(2)Ibn Jarir ya riwaito cikin hadisin Alqamata Bn Murthan, daga Sulaiman Bn Buraidata, daga babansa cewa;Annabi (S)ya isa Makkah sai ya tafi jikin wani qabari ya zauna a gurin yana khuduba, sannan miqe da hanzari ! Sai muka ce yaa Ma'aikin Allah , lalle munga abinda kayi. Yace;

‘’ NA NEMI IZNIN UBANGINA NE NA YIN ZIYARAR QABARIN MAHAIFIYATA, SAI YAYI MIN IZNI , SAI NA QARA NEMAN IZNINSA DON NA NEMA MATA GAFARA AMMA BAI YI MIN IZNI BA .‘’

Ba mu taba ganin kuka irin na wannan lokaci ba (in ji Buraidata ).

(3)- Ibn Abiy Haateem ya kawo cikin tafsiri nasa daga Abdullahi Bn Mas'ud yace;Wata rana Manzon Allah (S.A.W.W )ya fita zuwa maqabarta sai muka bi shi , muka je har ya zauna a wani qabari ya gana da shi na tsahon lokaci, sannan yayi kuka, muma mu kayi kuka saboda (ganin )kukansa , sa'an nan Umar Bn Khaddab ya miqe ya bi shi , ya kira shi sa'an nan ya kirawo mu yace; Kukan me kuke yi?Sai muka ce;Muna kuka ne saboda kukan ka.Yace;

‘’ AI WANNAN QABARI DA KU KA GA NA ZAUNA A WAJENSA QABARIN AMINATU NE, NA NEMI IZNIN UBANGIJINA NE DON ZIYARTARTA KUMA YAYI MIN .‘’

A cikin wata riwayar ta Ibn Ma'ud ya qaro da cewa, ‘’ NA NEMI IZNIN UBANGIJINA DON YI MATA ADDU'A AMMA BA AYI MIN BA. SAI AKA SAUKAR DA ‘’ Ba ya kasancewa ga Annabi da ma wadanda su kayi imani su nemawa mushirikai gafara....‘’ SAI IRIN ABINDA KE KAMA MAHAIFIYA (na tausayi )GA 'DANTA YA KAMA NI....‘’

(4)- 'Dabarani ya riwaito da isnadi zuwa kan Ibn Abbas, yace;Yayin da Annabi ya dawo daga yaqin Tabuka da kuma Umra .....

‘’ LALLE NA SAUKA A QABARIN MAHAIFIYATA NA ROQI ALLAH YAYI MIN IZNIN CETONTA RANAR ALQIYAMA AMMA SAI ALLAH YA QI YIMIN WANNAN IZNI, ITA TAUSAYINTA MAHAIFIYATA CE . SA'AN NAN JIBRILU YAZO MIN YACE, ‘’ Istigfarin Ibrahim (da ka ji ya yi )ga babansa (ba ta kasance ba )face wani wa'adi ne da muka yi masa, amma da ta bayyana gare shi cewa maqiyin Allah ne sai ya barranta daga gare shi .‘’

(Tafsir Ibn Kasir, J:2, SH:440 )

         TAMBAYA

- Shin, Kaddabi da Affan sun mutu suna musulmai ne?

- Yanzu a ina suke?

- Me yasa ba ku kawo mana makomarsu cikin littafai ba?

- Ashe za a iya bawa Annabi ceton iyayen wasu amma a hana masa na mahaifitarsa ko da ya tabbata haka?

- Ina wannan matsayi da Allah yace zai ba shi har sai ya gode?

          A.I.G

      09039791509

~30th May, 2020/ 9-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post