An shirya makirci domin hana Almajiran Shaikh Zakzaky gudanar da tunatarwa a Masallacin Fagge, Kano

An shirya makirci domin hana Almajiran Shaikh Zakzaky gudanar da tunatarwa a Masallacin Fagge, Kano.

An samu wasu bayanai dake tabbatar da shirin AZZALUMAI na son haifar da RIGINGIMU tsakankanin Yan'uwa na Kano wanda zai zame silar dakatar da Wakilin Yan'uwa na Kano wato Dr. Sunusi Abdulkadir daga yin TUNATATWAR da aka saba yi a duk bayan sallar Juma'a.

Bayanan sirrin sun nuna wasu sunyi zama a kano za ayi amfani da kirkirarrun makirce makircen da azzalumai ke haifarwa ne na, nan da can, Kuma da sunan rikicin cikin gida don hakakar da burin na su.

Asalin makircin sun so aiwatar da shi ne a cikin watan Ramadan donj fakewa da makircin da azzalumai ke kullawa a Abuja,, sai suka nemi goyon bayan mazaunin wata  Jiha  wanda kuma suka mayar dashi MAI FADA MASU SU JI, Shi kuma sai ya basu shawarar su bari sai bayan watan azumi sannan su aiwatar da shirin.

Kadan daga shirin da aka shirya a zaman shine, za su shigo Masallacin faggen da wuri inda Yan'uwa ke zama domin sauraron tunatarwa daga Wakilin garin , sai su hada kayan maganarsu, ta yadda Liman na kammala Sallah sai su fara Tunatarwa, ba tare da sun mika abin magana ga Wakilin Yan'uwa  Dr. Sunusi Abdulqadir ba.

Haka kuma dai, a zaman an tabbatar da lalle za ayi yamutsi a wannan Juma'ar, Amman sunce yamutsi na mako daya ne kawai. Daga nan kuma sai su kwace damar da ake amfani da ita wajan dora Yan'uwa bisa karantarwar Shaikh Zakzaky, yanzu sai abinda MASU FADIA MASU SU JI suka fada za a runka fadawa Yan'uwa.

Idan muka waiwayi baya kafin tawayiyya, Almajiran Shaikh Zakzaky (h) sun kasance suna yin tunatarwa ne a Masallacin Sarki,
daga baya aka dawo da tunatarwa Masallacin Fagge saboda fitinar yan Tawayiyya,

Haka kuma lokacin Mallam Muhammad Kabir Alkanawy aka shirya makircin mayar da tunatarwa biyu a cikin Masallacin Fagge har zuwa lokacin da Shaikh Turi yazo Garin amma basu daina ba  kuma sanadin barin Harka Kenan. .

Duk wadannan makirce makircen na haifar da matsaloli don hana Yan'uwa tunatarwa a Masallacin gidan Sarki har zuwa lokacin Mallam Kabiru Alkanawy da aka raba tunatarwar biyu da kuma yanzu da suke hankoron haifar da Wai hana Wakilin Yan'uwa Mallam Sunusi Abdulqadir gudanar da tunatarwar, makircin Azzalumai ne.

Abin mamaki basu daddara ba har yanzu suna mafarkin sake kawo matsalar da Wai za a hana Wakilin Yan'uwa na Kano , Dr. Sunusi Abdulqadir yin tunatarwa ga Yan'uwa kamar yadda aka saba.

Wannan dan rubutun hanunka mai sanda ne ga masu shirya makircin su san Almajiran Shaikh Zakzaky (h)  suna ankare dasu, Kuma in Allah ya yarda ba za suyi nasara ba, Kuma ba su Isa su kautar da hankali Almajiran Shaikh Zakzaky daga halin zaluncin da Buhari ke yiwa Jagoranmu. Shaikh Zakzaky da Mai Dakinsa  ba.

Idan yanayi ya bada za a bayyana  masu shirya wannan mummunan shiri.

Allah ya fito mana da Jagoranmu da Mai Dakinsa da sauran Yan'uwa da gaggawa cikin izzah da karama.

Buhari Free Zakzaky
Media forum kano

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post