==================
Bayan da rikicin addini ya barke a garin tun ranar alhamis 14/5/2020 zuwa jiya juma'a 15/5/2020,
Wanda yajawo asaran rayuka da kuma kona dukiyoyi masu dinbin yawa,
Tinno garine mai tarin arzikin gona musamman shinkafa, mutanen garin sukanyi noman shikafar rani data damina,
kamar yadda mazauna garin suka shaida mana cewa har zuwa yau shinkafa naci da wuta,
matasan garin sun taka rawar gani wajen kare kansu da mutuncinsu da dukiyoyinsu,
I zuwa yanzu babu labarin kashe wani almajirin Sheikh Zakzaky, haka zalika Fudiyyar garin nanan lafiya kalau,
Idan ba'a mantaba irin wannan ya taba faruwa a zamanin Janar Ibrahim badamasi babangida, a shekarar 1990, inda aka maida garin kufayi, wanda har kafafen watsa labarai suka ruwaito cewa anyi amfani da nakiyoyi a lokacin fadan,
Ya zuwa yau asabat mazauna garin sun shaida mana cewa sunyi jana'izar mutum 34, sannan masu munanan raunuka wadanda baza a iya shawo kansu ba, an kaisu asibitin Gombe,
Allah ya kiyaye gaba.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya
