@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @
TSIROWAR BISHIYA A GURIN DA YA YADA ZANGO
An riwaito daga Hindu 'yar Jauni tace,
‘’ Manzon Allah (S.A.W.W )ya sauka a wajen 'yar'uwata Ummu Ma'abbadin har ya dan kishingida a cikin bukkarta, a yayin da ya farka sai ya nemi a kawo masa ruwa, sai ya wanke hannayensa ya kuskure bakinsa, sannan sai ya tofar da ruwan a gindin wata 'yar qaramar bishiya da take kusa da gindin wannan bukka. Kawai sai muka wayi gari muka ga wannan 'yar shuka ta zama wata qatuwar bishiya mafi girman bishiyoyi, kuma ta fitar da wasu 'ya'yaye manya-manya kamar Ambar , kuma zaqinsu kamar dandanon zuma farar saqa.
Babu wani mayunwaci da zai ci wannan itaciya face sai ya qoshi ko mai qishirwa face sai ya qoshi , idan marar lafiya yaci 'ya'yan ta nan-da-nan sai ya warke, kuma babu wata raquma ko akuya da za taci ganyen wannan itaciya face sai amga hantsarta ta cika da nono kuma tayi qiba ta zama mai albarka .
Da yawa mutanen qauyen suke zuwa tsinkar wannan bishiya don yin magani ga marasa lafiyarsu kuma suyi guzuri mai yawa da ita .
Wata rana bamu ankara ba sai muka ga duk 'ya'yanta sun zube, ganyenta kuma duk sun zama qanana, sai hankalinmu ya tashi da ganin haka. 'Yan kwanaki kadan sai muka sami labari cewa ashe Annabi (S.A.W.W )yayi wafati.
Ana nan ana nan cikin wannan hali bayan shekara talatin (30)sai muka ga bishiyar nan daga qasa zuwa sama ta zama bishiyar qaya, kuma 'ya'yanta suka zube ta daina yin fure, bamu ankara ba sai muka ji an kashe sarkin muminai Aliyu B n Abidalib (R.T.A ), tun daga nan bata sake yin 'ya'ya ba , sai dai ganyenta kadai muke amfana.
Ana cikin wannan hali sai ga wani jini yana bulbulowa daga jijiyoyinta kuma ganyenta gaba daya ya zube , sai nan na hankalinmu ya tashi . Sai muka sami labari cewa an kashe Hussaini Bn Aliyu Bn Abidalib , daga sannan bishiyar ta mace gaba daya !‘’
Malaman tarihi sun kawo cewa Ummu Ma'abbadin da mijinta da dan'uwansa sun muslimta sunyi hijra zuwa Madinah.
✍🏻 ADO ISAH GUDA
09039791509
~16th May, 2020. KU KARANTA
WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
