Na Gode Allah Da Yayi Ni Musulmi Ɗan Shi'a – Cewar Malam Ado Isar Guda



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BA LAIFI BANE KA FADI BAIWAR DA ALLAH YAYI MAKA

Dukiya da 'ya'ya ado ne daga rayuwar duniya in ji Allah , duk wanda Allah ya ba shi dukiya da 'ya'ya to, ya sami babban kayan ado a duniya, amma ta wata fuska fitina ce gare shi.

Allah (T )ya tabbatar mana da haka inda yake cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

" ABIN SANI DUKIYOYINKU DA 'YA'YANKU FITINA CE GARE KU...."

Saboda haka samun kanka cikin musulmi kuma dan shi'ah mabiyi ko me wilaya ga iyalan gidan Annabi (S.A.W.W )ta fi dukkan wani abinda za ka samu na duniya .

Wannan dalili yasa naga ya dace na fito na nuna godiyata ga Allah ta hanyar bayyanawa mutane ni wanene.

NI DAI MUSULMI NE 'DAN SHI'AH MABIYIN SAYYID IBRAHIM EL-ZAKZAKY (H )ME WILAYA GA AHLUL-BAIT JINGIN TSIRA WANDA ANNABI (S.A.W.W )YA UMARCE MU DA MU RIQE SU A MATSAYIN JAGORORI BAYANSA.

Ba bisa fahari nake furta wadannan kalamai ga sauran 'yan'uwanmu musulmi ba, sai dai kawai yin koyi da Annabi (S.A.W.W )inda yake cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

" An bani abubuwa biyar wadanda ba a bawa wani Annabi gabannina ba , kuma ba ina fadin hakan bisa fahari bane. An aiko ni zuwa ga mutane gaba daya fararen (fata )da baqaqe, an hore min kallon (abinda ke nesa )na tsahon tafiyar wata guda , kuma an halatta min ganima wacce ba a halattawa wani gabannina ba, kuma an sanya mi (dukkan fuskar )qasa (a matsayin gurin yin )sujada kuma mai tsarki , kuma aka bani ceto (na wanda naso ), sai na jinkirta ta ga al'ummata (zuwa )ranar alqiyama , kuma ita (ceton )na wanda bai yiwa Allah shirka bane ."

(Musnad Ahmad, J:1, SH:301)

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~24th May, 2020/ 3-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post