Ma'aunin Tantance Hadisan Ƙarya Da Na Gaskiya!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

LITTAFAI CIF SUKE DA HADISAN QARYA

Duk ma'abocin karatu zai riqa cin karo da hadisai masu buga qwaqwale, domin za ka ji su sun fi kama da hauka fiye da hankali. Yawancin irin wadannan hadisai an samar dasu ne don wanke miyagun ayyukan wasu tare da nemo falalar qarya ga wadanda ba su da su.

Wannan dalili yasa aka qirqiro irin wadannan hadisai ana jingina su cewa wai daga Annabi (S.A.W.W )ne, alhali qarya akayi masa, kuma wadannan hadisai na nan cif cikin littafan da ake kira sahihai .

Sanin irin wadannan qarerayi za su faru yasa Manzon Allah (S.A.W.W )ke cewa, " DUK WANDA YAYI MIN QARYA DA GANGAN, TO, YA TANADI MAZAUNINSA A WUTA ."

MATAKAN GANE HADISAN QARYA

Mafi girman hanyoyin guda biyu ne, ga su kamar haka:-

(1)- Annabi (S.A.W.W )na cewa;

" DUK WATA MAGANA DA AKA KAWO TA AKA CE DAGA GARE NI TAKE , TO, KU AUNA TA DA LITTAFIN ALLAH . IDAN KU KAGA TA YI KARO DA LITTAFIN ALLAH KU AJIYE TA, BA DAGA GARE NI TAKE BA (Malamai ne suka fada )."

(2)- Imam Ahmad yace, baban Amir ya bamu labari, shine Aqdiy Abdul-Malik Bn Amru, Sulaiman ya bamu labari , shine Ibn Bilal daga Rabi'ata dan baban Abdurrahman , daga Abdul-Malik Bn Sa'id , daga baban Humaid da baban Usaid (R.A )cewa, Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

" Idan ku kaji wani zarce cewa daga gare ni ne wanda zukatanku suka san shi, kuma gashin ku da gangar jikin ku suka nutsu da su, kuma ku kaga wannan abu ya kusanta gare ku (saboda kyawunsa ), to, ni na fi cancanta da shi fiye da ku. Kuma idan ku kaji wani zance cewa daga gare ni ne, amma zukatanku na qyamatarsa, kuma gashinku da gangar jikinku na gudunsa, kuma kuna gani wannan abu abin nisanta ne gare ku, to, ni na fi ku nisanta da shi ."

(Musnad Ahmad , J :3, SH:497)

Saboda haka batun isnadi (chain of transmission )ba shine babban ma'auni ba, domin da irin wadannan isnadan aka inganta hadisan qarya aka qaryata hadisan gaskiya .

Allah yasa mu amfana.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~24th May, 2020/ 3-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post