Kada Ka Ruɗi Kanka Da Cewa, Laifin Ɓatar Da Mutane Akan Shugabanni Yake !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SU MA KANSU BA SHIRYAYYU BANE BALLE SU SHIRYAR DA KU

An dade ana yin ruwa qasa na tsotseway, ba a fasa ba kuma ita ma ba za ta fasa tsotsewa ba matuqar yana zuba a kanta.

Tun zamanin Manzon Allah (S.A.W.W )ake karantar damu Qur'ani ba tare da qaro wani abu sabo ko tauye wani abu daga cikinsa ba, amma har yanzu an kasa fahintar haqiqanin darusan da ke cikinsa . Hanyoyin dai guda biyu ne, kuma babu wacce aka boye mana komai nata ba tare da an nuna mana khairi da sharrin da ke cikinta ba.

Matuqar azzalumi ko kangararren malami zai kira ka zuwa ga bata kai kuma ka bi shi, to, ba zai taba nuna maka daidai ba har sai lokacin da ka soma kangarewa umarninsa .

Mutane sun dade suna kuka game da yadda shugabannin nan ke jujjuya su kamar qwallo, sai sunyi kamar za su gane, amma sai ka ji suna cewa;

‘’ TO, AI DUK ABINDA SU KAYI LAIFI NA KANSU, MU NAMU KAWAI BIYAYYA CE TUNDA SHUGABANNINMU NE .‘’

To, ku bar rudar kanku, domin wannan ba zai taba zama uzuri karbabbe wajen Allah ba .

Nazarci wannan aya sosai cikin nutsuwa.

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Kuma suka bayyana ga Allah gaba daya (shugabanni da mabiyansu ), sai raunana (mabiya )suka cewa wadanda suka kangara (shugabanni ), ‘’ LALLE MU MUN KASANCE MASU BI A GARE KU (a duniya ), TO, SHIN, KU MASU WADATAR DAMU NE GA BARIN WANI ABU NA AZABA?‘’ Suka ce;

‘’ Da Allah ya shiryar damu da (mu ma da)mun shiryar da ku (amma mu ma kanmu batattu ne ), duk daya ne a kanmu (mu da ku ), muyi raki (rashin jurewa wannan azaba )ko muyi haquri (cikinta )ba mu da wata mafita .‘’

  (IBRAHIM, AYA TA 21)

Saboda haka in ka shirya jure azabar Allah sai ka cigaba da bin su kan bata kamar yadda ka ji daga bakunansu .

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~23rd May, 2020/ 2-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post