Mu'ujizar Annabi (S.A.W.W) Ta Bayyana Yayin Hijirar Sa.. (1)




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SAUKARSA (S.A.W.W )A RUMFAR UMMU MA'ABADI

Ummu Ma'abadi wata mata ce 'yar qabilar Khuza'iya wacce ke zaune a hanyar matafiya tsakanin Makkah da Madinah, aikinta shine ciyar da matafiya ko shayar da su.

Cikin wannan shekara ta hijra anji wani fari mai tsanani . To, a hanyarsa ta tafiya (S.A.W.W )sai ya ratse ta Bukkar wannan mata don ta sayar musu da nama ko nono , amma basu samu ba.

Cikin wannan yanayi sai Manzon Allah (S.A.W.W )ya hango wata ramammiyar Akuya wacce ta kasa bin 'yan'uwanta kiwo saboda wahala da yunwa .

Sai ya tambayeta cewa ko za a sami nono a jikin akuyar, sai matar tace ba za a sami komai tare da ita ba, sai yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ KIN YIMIN IZININ NA TATSETA A HAKA ?‘’

Bayan tayi masa izni sai yace ta ba shi qwarya, da ta kawo masa sai ya harde wannan akuya ya kama hantsarta da hannayensa mai albarka ya ambaci sunan Allah ya fara tatsar nonon har sai da ya cika qwarya, ya bawa jama'ar dake wannan guri kowa yasha ya qoshi sannan shi ma yasha . Sai kuma ya qara tatsa cikin qwarya guda ya barwa masu akuyar. Tun daga wannan rana mutanen qauyen suka riqi wannan rana RANAR WUCEWAR WANI MUTUM MAI ALBARKA .


Bayan mijinta wannan mata ya dawo ta bashi labari sai yace; ‘’ Wannan ai ina kyautata zaton mutumin nanne na larabawa , da zan hadu dashi da na bi shi .

Ita kuwa wannan akuya ta cigaba da rayuwa ana tatsar nononta har lokacin mulkin Umar Bn Khaddab sannan ta mutu .

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH .

Tare da Ado Isah Guda .

          09039791509

~15th May, 2020. KU KARANTA 

WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post