Firgici ko Rashin tabbas???




```Ma'asumah Nigerian News Update```


Daga dabi'ar dan Adam akwai tabbatawu da hasashen dorewar abin so da kuma kauna, a kasin haka ga abin ki ko kyama.


Rayuwar nan na daga cikin babbar kyauta da Allah ya yi ma dan'Adam ba ko shakka, to a haka ne zamu cigaba da rayu?


Cikin rashin tabbas da firgici ba wai na rasa dukiya, mutunchi ko 'yanci ba. A'a na rasa dukkan rayuwar gaba daya cikin kaskanci da firgici.


Rayuwar mu kamar a daji take idan ba kayi fada a kanta ba zaka dawwama cikin gudu da firgici.


Mutuwar taana ko mutuwar mazuru zaka zaba dan Nijeriya. (Mutuwar biyayya ga makasa ko tashi tsaye gurin yakar makasa ka rasa kanka).


Shin wai dan Nijeriya ya manta cewa ita rayuwar kaskanci ko ta 'yanci cikin zukar jini ake yin ta.


Shin rayuwa saman gwuiwowi zamu yi da sinsinar takalma abokan hallita ko tsintar ababen da suka gama amfani da su kamar karnuka.

Ko kuwa zamu tashi ne mu zama a kan duga-dugan mu yayin fafutukar neman 'yancin Rayuwa.


Idan ba kai ba! Wa zai Iya?

Idan ba yanzu ba, Yaushe ne lokacin?

5152020
AhmmarSabo

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post