Madalla Da Irin Wannan Halin Da Sayyid (H) Ke Ciki!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

IRIN WANNAN HALI MA'AUNI NE NA GANE MATSAYIN MUTUM WAJEN UBANGIJINSA

Baki (mouth )abu ne wanda ba a yi masa shema, ko nace ba a katange she, saboda haka zai iya kaiwa duk inda ya nufa da zuwa.

Wani lokaci ya kai mutum wuta ko aljannah , ko kuma ya kai wani mutum zuwa wani madaukakin matsayi wanda Allah bai kai shi ba, kuma ko da ka yi masa musu wasu za su gaskata shi.

Irin wannan dabi'a ta baki (harshe )tasa a tarihi aka riqa fifita wasu qasqantattu kan madaukaka , aka qasqantar da masu daraja zuwa mafi qasqancin qasqantattu , sai dai kuma ba anan take ba.

Alqawarin Allah ne zai jarraba bayinsa muminai don ya daukaka matsayinsu zuwa madaukakin matsayin da tunani ba zai iya hango shi ba.

Wannan dalili yasa aka jarrabi Annabawa, A'imma (A.S )da kuma mujaddadai don su zama wani alami na gane mutanen kirki da ke kan gaskiya .

Yanzu duk wanda ka ji yana da'awa amma irin abinda ya sami magabatansa na cutarwa bai same shi ba, to, ka nisance shi, domin shi kansa ba shiryayye bane balle ya shiryar da kai.

Annabi (S.A.W.W )na cewa ;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Na rantse da wanda raina ke hannunsa, Allah ba zai hukunta mumini da wani hukunci ba face ya zama alkhairi gare shi, idan wani farin ciki ya same shi sai ya gode, ya kasance alkhairi gare shi. Kuma idan cutarwa ta same shi sai yayi haquri , ya kasance alkhairi gare shi. Amma fa hakan ba ta faruwa ga wani koma bayan mumini .‘’

 (Muslim , J:8, SH:227)

Irin hakane ta faru ga Annabi Ayuba, Yusuf, da Muhammad (S.A.W.W ), kuma alkhairi ne ya same su a qarshe .

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509
~28th May, 2020/ 7-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post