Ayyuka Huɗu (4) Masu Gaggawar Kai Mutum Aljannah!!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DA YAWA DAGA CIKIN MUTANE NA YI WASA DASU 

Aikin alkhairi abu ne wanda ba kowa ne ke damuwa da aikata su ba, duk da cewa sunfi sauqi fiye da aikin banza.

Tasirin shaidan ne kan dan adam a duk lokacin da yaga zai aikata aikin alkhairi sai ya sanya masa shakku da kasala, amma a aikin sabo sai ya qarfafe shi.

Manzon Allah (S.A.W.W )ya umarce mu da aikata sauqaqan ayyuka wadanda za su kaimu aljannah , amma mun kasance masu yin watsi da su. Ga maganar nan cikin hadisin da ke biye;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ YAA KU MUTANE, KU RIQA WATSA SALLAMA (a tsakaninku yayin haduwa ), KUMA KU CIYAR DA ABINCI (ga mabuqata ), KUMA KU SADAR DA ZUMUNCI (cikin dangi da 'yan'uwa na addini ), KUMA KUYI SALLAH CIKIN DARE YAYIN DA MUTANE KE BACCI , ZA KU SHIGA ALJANNAH DA AMINCI .‘’

  (Musnad Ahmad, J:5, SH:451)

Amma abin mamaki sai kaga mutum ya ga dan'uwansa maimakon yayi mar sallama sai ya kawar da kansa daga gare shi, ko kuma ayi masa sallama ya qi amsawa.

Ciyar da abinci ga raunana ta zama tamkar tara (tax )ake yiwa mutane , zumunci kuma an barwa FULANI , domin su suka fi dukkan wasu qabilu qoqarin sada zumunci.

Sallar dare kuwa da zama sai lokacin da mutum ke neman buqata ta gaggawa wajen Allah sannan kaga yana yinta, amma ba zai yi don neman yardar Ubangijinsa ba.

ALLAH YASA MU AMFANA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~28th May, 2020/ 7-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post