`Ma'asuma Nigeria news update.
-Imam yace musiba ga wanda ya jure guda ɗaya ce, ga wanda kuma bai jure ba guda biyu ce, wato musibar da kuma radadin rashin dauri yar acikin zuciya.
-Imam yana cewa taimakonka ga raunana yana daga cikin mafificiyar sadaqa.
-Imam yace yawan damuwa da kuma baƙin ciki yana haifar da saurin tsufa.
-Imam yace rikon amana da kuma Faɗin gaskiya, suna janyo arzuki, yin karya da kuma yaudara suna janyo talauci da kuma munafunci.
-Imam yace mutun bai samun ladar musibar da allah T ya jaraba shi da ita face sai idan ya daure kan musibar.
-Imam yace kyakkyawan makwabtaka ba itace kawai kamewa daga cutar da makwabci ba, a'a itace daurewa daga cutar war makwabci.
-Imam yace na hore ku da yin addu'o, domin addu'a tana tunku de bala oi.
-Imam yana cewa duk wanda ya fara addu'a batareda soma yabon Allah T ba, Dakuma yima manzon Allah salati ba to kamar wanda yayi harbi ne da gwafa ba dutse.
-Duk wanda yakasance mai tattali to ba zaiyi talauci ba.
-Imam yace ku nemi ilimin addini saboda shi ilimi mabudin basira ne kuma dalili na zuwa ga madaukakan darajoji.
#Abbakar Labbo.
#Public health concern.