🇳🇬 *MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES*
Tare da Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare 070-32803940
Ba tare da bata lokaci ba na zabi na rubuta wannan wasiqar ne ga 'yan'uwa bisa a irin wannan halin da muke ciki na waki'a mai tsawo haka, don kuwa har ya zuwa yau muna cikin waki'a ne kuma kullum qara muni take sabida yanda dukanmu muna sane da halin da Jagora yake ciki, masoyinmu masoyin al'umar wannan qasa tamu Nijeriya dama al'umar duniya gaba daya! Yana tsare sama da shekaru hudu da shi da Ummah Zeenah Uwargidansa cikin mummunan yanayi na rashin lafiya! Ya isheka in aka ce maka suna tsare har yanzu dukansu da harsasai a jikinsu, harsasai masu guba da Sojojin Qasarnan bisa Umarnin Buhari (L) suka harbe su dasu, don son ganin bayansu ba tare da sunyi musu lefin komi ba, bayan kashe masa 'ya'ya hazikai har guda shida a gabansa, tare da kashe masa almajirai sama da dubu wa 'yanda suka hada da jarirai da yara qanana da Mata da Dattijai da Samari da manya magidanta, Kai harda zuriya gaba daya sun qarar dasu ba bisa lefin komi ba. Ta hanyar mummunan nau'in kisa kala-kala na qeta da rashin Imani, e.g kamar qona mutum da wuta da ransa, da harbin Mai ciki ta haifu a take a kuma harbe jaririn da ta haifa! Da Kona Mata da Jarirai da da wuta da ransu wanda ko dabbobi Mai Imani bai dace ya yi musu irin wannan kisa ba! Amma aka yiwa Bil'adama haka! An yi musu wannan kisa ne ba don komai ba sai don sun ce su basason wannan tsarin mulkin turawan Yammah, Wanda Allah ya yi hani da biyayya gareshi inda Allah yace a Al-Qur'ani *"Summa ja'alnaka ala Shari'atin minal Amri Fatta bi'aha wala tattabi ahawa'al lazina la ya'alamun"* Fassara *"Sannan mun sanyaka akan shari'a game da kowane al'amari kabi kada kabi soyace-soyacen zuciyar wa'yanda basu da Ilimi"*
Wannan soyace-soyacen zuciyar wa'yanda basu da Ilimi dinnan kuwa da Allah ya hanamu bi shine "Constitution" da duk wani abu da ya sabawa fadar Allah data Manzon sa, da duk wani abu daya sabawa Qur'ani, Allah bai yadda kayi masa da'a ba!
Wannan dalilin ne yasa suka far masa shida almajiransa kamar yadda Kafirai suka farwa Manzon Allah a Makkah da ya yi qira azo abi Allah abar bin Lata da Uzzah.
Sak babu banbanci Manzon Allah bai bisu ba sun far masa gashi Sayyid Zakzaky shima bai bisu ba shima sun far masa!
Insha Allah kamar yadda Manzon Allah ya yi Nasara hakama Sayyid Zakzaky zai yi nasara. Qiran iri daya ne bai kuma boyuwa kowa ba!
Suna tsare dashi duda hukuncin kotu da tayi na a sake shi! Wannan wane irin zalunci ne!?
YAN'UWA zan yi magana ne akanku bisa wasu kurakurai da muke ta tafkawa, zan yi magana ne akan wasu wa 'yanda suka yi qarfi har suna neman samun wajen zama! Wa 'yanda da yawa basu ma dauke su a bakin komi ba!
Amman suna cutar da Qiran da Sayyid yake yi gayar cutarwa! Wasu suna yi ne bisa rashin sani wasu kuma daman aikin da aka basu kenan! Wato Jami'an cikinmu da Gwamnati ta dasa! Ta basu aikin wargaza qiran.
Abu na farko dazan yi magana akan shi shine game da mu'amulantar al'ummah da muke yi Musamman bayan wannan harin Gwamnati garemu!
Da yawanmu mun bi son zuciyar mu!
Wanda Sayyid ya nuna mana a aikace yanda za muyi, amman mukaki yi! Munayin abinda ya yi mana dadi wanda hakan yana cutar da qiran ne, yana sake temakawa maqiya ne!
Wannan abun shine bayyana fishinmu a fili ga su masoyan maqiyanmu wa 'yanda suka zalincemu ta hanyar mayar musu maganganu marasa dadi duda sun fada Mana marar Dadi!wasu maganar ma da wasu suke mayar musu basu dace ma'abocin addini mai qira ga azo abi Allah dan Gwagwarmaya ace yana furta su ba!.
Wa 'yannan mayar da maganganun marasa dadin ji din in suka yi mana, basu taba amfanar da wannan qiran ba! Ya zamana cewa da yawa mun kasa hadiye fishinmu yanda ya kamata!
*Gashi kuma muna gani a aikace yanda Sayyid Zakzaky ya yi duda abinda suka yi bai fasa yi musu alherin da yake yi musu ba, sai ma ya sake nunkawa, harma yace a fara bawa wa 'yannan wa 'yanda da hannunsu da temakonsu, sun kuma fito fili sun nuna gabarsu sosai a fili gareshi, da hannunsu aka zalunce shi, zalunci wanda ba a taba yiwa wani bil'adama ba a doron qasa, Amma yace a Fara basu, bai hanasu ba Kuma bai bisu da mummunan magana ba duda Girman nau'in zaluncin da suka yi masa, yace a Fara dasu!*
Ya bisu da alkhairi da fata nagari da kyautatawa a kullum!
*Wanda hakan ba qaramar cigaba da nasara ya kawowa harqa ba da ma'abotanta ya qara Kuma tabbatar mana da cewa shi Sayyid Zakzaky lallai magajin Annabi ne don sak irin abinda da Annabi ya yi shima ya yi, ga duk wanda ya zalunce shi yana saka masa da alkhairi ne bada mummuna ba haka Sayyid ma ya yi. mungani ya kasance! Ya saka musu da Alkhairi bayan zaluntarsa da suka yi.*
Mi yasa mu baza muyi koyi da Sayyid ba!!?
Da munyi kamar yadda yake yi ga wa wa'yanda suka cutar dashi suka Kuma goyi bayan masu cutar dashi Yana saka musu da alkhairi da ba a wannan marhalar muke ba da munjima da wuceta! Muna da damar gyarawa mu gyara 'yan'uwa muyi irin yanda Sayyid Zakzaky ya yi. Mu danne fishinmu mu zama masu kyautata musu! Da yawansu rashin shina ne! Wasu kuma Jami'an Gwamnati ne abinda suke so kenan, su mayar da mummuna sai ya zama ansamu rigima tsakaninmu da su al'umar qasar su gagara gane gaskiyar qiran da Malam din yake! Sai ai ta jayayya da cacar baki kawai!
*Mu gyara musamman a wannan lokacin da al'ummah ta Fara Gane zaluncin wannan Gwamnati, mu zama masu kyautata musu da haquri da halinsu*
Mu tuna da wannan qissar da Sayyid Zakzaky ya taba bamu shekaru da dama da suka wuce a Garin Kudan! Bayan ta'addancin maqiya ga 'yan'uwa a Garin na Kudan yanda Sayyid Zakzaky ya bamu wa 'yannan Qissosi kamar haka;-
*QISSA TA FARKO*
"Wata Rana Matar Abu lahabi ta tauko gaushin wuta da yawa a cikin kasko Manzon Allah yana Sallah akan in ya yi Sujjada sai ta kifa masa akai! Ta taho kenan sai Allah ya yi ikonsa qasa ta qurmudar da qafarta ta fadi wutar zata zube Mata a kanta a qirjinta Manzon Allah yana Sallah sai ya yi wuf ya yanke Sallah din da yake, yaje ya temaketa ya kautar da wutar a jikinta bata zube Mata a kanta ba, Bata cutar da ita ba, Yana tambayarta shin bakiji ciwo ba koh!? ta amsa da eah"
Kujifa 'yan'uwa Manzon Allah Sallah yake fa ya yanke ya temaki wacce tazo cutar dashi!
Kunsan kuma irin Sallar Manzon Allah ba irin tamu bace ba, amman duda haka ya yanketa ya barta a temakon wacce tazo cutar dashi Kuma kullum tana cikin yi masa mungun qulli na cutarwa ga kuma gayar tsana iya tsana ta qarshe ta tsane shi amman ya yanke Sallah ya temake ta! Ina kuma gamu don Allah kayi tunani, muma Kuma a irin halin da muke ciki kenan! Wannan matakin ne kuma mafitar da za ta bamu nasara sosai! Mu temaki raunana da wa 'yanda ake Yaudara!
*QISSA TA BIYU*
Mu qara tuna wannan qissar ta wani kafiri da kullum bashi da wajen zuba shara sai qofar gidan Manzon Allah don Saboda qiyayya da yake yiwa Manzon Allah sabida shi burinsa ya baqantawa Manzon Allah! Amman haka Manzon Allah da kansa yake debe sharar a kullum in wannan kafirin ya kawo ya zuba! Manzon Allah bai taba yi masa magana ba! Kuma ya hana ayi masa magana ko a dauki mataki a kansa! In yazo ya zuba, sai Manzon Allah ya debe da kansa haka kullum.
Har wata Rana sai bai zo ya zuba ba Manzon Allah ya tambaya yana ina ne!? aka ce masa ai yana Gida bai da lafiya! Manzon Allah da kansa yaje ya dubashi ya yi masa goma ta arziqi! Wannan dalilin yasa ya musulunta! Muma in muka zama haka ga wa 'yannan al'ummar da dayawa sun rabauta!
*QISSA TA UKU*
Mu kuma qara duba abinda da aka yi masa a da'ifa yaje qiransu zuwa ga Addinin Allah suka sa yara suka yi ta jifansa da duwatsu suka yi masa kaca-kaca da jini suka fasa masa kai sosai (wa'iyazubillah) har sai da Gemunsa ya jiqa da jini! Tafin qafarsa shima ya jiqe da jini! Mala'iku masu ikon tasarrufi da Allah ya basu na abubuwa kamar Ruwa da Iska da Duwatsu da Qasa da Sauran su, suka zo daya bayan daya kowannen su, suka nemi izinin Manzon Allah akan ya basu dama su hallakar dasu gabadaya amman Manzon Allah ya yi haquri ya yi, har a cikin Maganarsa yace basu sanshi bane ba shiyasa suka yi masa haka da sun sanshi baza suyi masa haka ba da sannu kuma za su sanshi, shi an aiko shi Rahama ne ga talukai, yace a rabu dasu.
Yan'uwa mu duba mu gani, wa 'yannan abubuwan sun yi dai-dai da yanayin da muke ciki, haquri za muyi da mutanenan har yanzu muna marhalar da'awa saura kadan mu qara gaba suwa mar hala ta gaba Amman yanzu kam muna marhalar da'awa ne! Juriya zamu yi sosai juriya ta Gaske.
Da yawa basu fahimce mu ba har yanzu, yanzu ne lokacin da in muka jure muka kyautata musu, muka yi haquri da cutarwar su da wautarsu da yawa za su rabauta.
Mu yi koyi da Manzon Allah da Sayyid Zakzaky yanda suka jure suka cije duda tsananin cutarwa ta maqiya.
*Mu dena munana maganganu garesu da kuma shuwagabanninsu hakan na cutar da Harqa Yana cutar da Manzon Allah da Sayyid Zakzaky Yana cutar da qiran Sayyid Zakzaky!*
*Hakan yana amfanar maqiya ne! Ba a hana magana ba da mayar da martani ba! Amman mu rinqayi cikin hikima da balaga da fasaha mufa mabiya Imam Ali ne fa ko mun manta ne!*
Allah ya ce *"Uddu'u ila sabili rabbika bil hikimati wal mau'izatul hasanah"* Fassara *"Ka yi qira zuwa ga hanyar Ubangijinka da Hikima da wa'azi Mai kyau"*
Amman abinda muke yi na biye musu baya amfanar damu da ita harqar sai dai iya qara temakawa maqiyanmu ne!
In muka gyara wannan toh tabbas za muga canji fiye da wanda muke gani yanzu! Hakama da ace mun gyara da wuri tuntuni da yanzu ba a wannan marhalar muke ba da tuni mun wuce ta!
Muhadu gobe a rubutu kashi na biyu
Ga number ta don gyara ko shawara 070-32803940.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
*FREE ZAKZAKY DA UMMUNAH ZEENAH DOLE*Ku ziyarce mu ta wannan link din www. Ma asumah.com.ng don samun sabbi da ingattattun labarai! Da kuma abubuwa masu amfanarwa anan duniya da lahira.
Tags:
Muhimman zantuka