Ayoyin Dake Kuɓutar Sa Mahaifan Annabi (S.A.W.W) Daga Wuta!!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ALLAH YA KUNYATA QARYAR KU MIYAGUN MALAMAI

Annabi (S.A.W.W )masanin gaibu wanda yasan abinda za ayi a bayansa, shi yasa ya riqa gargadinmu ta hanyoyi dabam-daban.

Saninsa kan cewa za a qirqiro qarerayi a bayansa don lullube gaskiya da bayyanar da qarya yasa yace mana duk abinda ake ce mana daga gare shi ne, to, mu auna maganar da ayoyin Allah mu gani, idan sunyi karo, to, qaryarsu ce ba daga gare shi bane . Kuma yace ga masu qirqirar qarya cewa su tanadi mazauninsu a wuta.

Mun kawo hadisai cikin littafan sunnah masu cewa mahaifan Annabi (S.A.W.W )'yan wuta ne, amma ku qara biyo mu cikin rubutunmu .

GA AYOYIN DAKE QARYATA MAGANARSU

Allah (T )na cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

(1)- ‘’ INNAH QAD UHIYA ILAINA ANNAL AZABA ALAH MAN KAZZABA WATAWALLAH ‘’ lalle anyi wahayi zuwa gare mu cewa, azabar Allah na tabbata ne akan wanda ya qaryata (gaskiya )kuma ya juya baya.‘’

(2)- ‘’ WAMAH KUNNAH MU'AZZABEENA HATTA NABA'ASA RASUULAH ‘’ Mu bamu kasance muna yin azaba (ga wani ba )har sai mun aiko da Manzo .‘’

          NAZARI

Idan muka nazarci wadannan ayoyi dole muyi tambaya cewa:-

(i )- Su mahaifan Annabi (S.A.W.W )sun qaryata waye, kuma wa suka juyawa baya da azabar Allah za ta shafe su?

(ii )- Wanne Manzo ne aka turowa mahaifan Annabi (S )da har za muce sun qaryata shi?

Mahaifansa (S )sun rayu ne kuma suka rasu a lokacin fatara (lokacin )Annabi Isah (A.S )yayi wafati, kuma Muhammad (S.A.W.W )bai zama manzo ba.

To, bisa wacce hujja ce za ku kai mahaifansa wuta?

Daga wakilanmu ns Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~31st May, 2020/ 10-10-1441.

KU  KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post