Allah Ya Qara Juriya Da Sabati Ga Ƴan Abuja Struggle!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

WANDA YA CIYAR YAYI YAQI KAFIN NASARA BA ZAI ZAMA DAIDAI DA WANDA YAYI DAGA BAYA BA

Dole ayi jinjina ga duk wanda ya sadaukar da lokacinsa, dukiyarsa, lafiyarsa da kuma ransa don gani jagora ya sami 'yanci .

Tabbas, fitowa fili a shelanta zaluncin azzalumai da nuna bara'a gare su ya fi isar da saqo fiye da komai, domin haka Manzon Allah(S.A.W.W )yayi ga kafirai yayin da suka nuna cewa su da muslimci za suyi fada.

Duk wanda zai taka rawar gani ta kowacce fuska don ganin addini ya sami daukaka , to, ba zai taba zama daidai da wanda sai bayan nasara zai fito ya bada gudumowa ba, sai dai kowannensu Allah yayi musu alqawarin kyakkyawan lada.

INGANTATTUN HADISAI DAGA ANNABI (S.A.W.W )

(1)- Anas Bn Malik yace, Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

‘’ Lalle a cikin Madinah akwai wasu mutane (ba dukkansu ba ), babu wani tafki da za ku tsallake (ta cikinsa ), ko wata tafiya da za kuyi face suna (nan )tare da ku .‘’

 Suka ce, ‘’ Alhali suna Madinah (sunyi likimo )?‘’ Yace;

‘’ EH, UZURI NE YA TSARE SU .‘’

(Bukhari , J:4, SH:31).

(2)- Imam Ahmad yace, Waki'i ya bamu labari , A'amashu ya bamu labari daga baban Sufyan , daga Jabir yace, Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

‘’ Haqiqa kun bar wasu mutane (zaune )cikin Madinah , babu wani tafki da za ku tsallake , ko wata tafiya da za ku yi, face sunyi tarayya da ku cikin lada, rashin lafiya ce (kawai )ta tsare su.‘’

(Musnad Ahmad , J:3, SH:300 )

Ibn Majah ma ya fitar da wannan hadisi daga A'amashu cikin sahihi nasa .

(Ibn Majah, J:2, SH:923

‘’ ABIN SANI KAWAI ALLAH NA KARBA NE DAGA MASU TAQAWA .‘’

        (Qur'an )

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

       09039791509

~30th May, 2020/ 9-10-1441.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post