Kowa Yayi Ta Kansa, Wanda ya Ɓace Bazai Cutar Dashi Ba!!!




@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @

KA NEMI SHIRIYA KAWAI WAJEN UBANGIJINKA

A ko da yaushe burin mai addinin gaskiya shine neman yardar Allah cikin dukkan ayyukansa . Da ace mutum zai yi aiki sannan a qarshe bai sami yardar Allah ba, to, da wannan aiki nasa ya zama aikin banza.

Yardar Allah cikin addini ba zai taba samuwa ba har sai mutum ya tsarkake ayyukansa , kuma ya nisanci hangen laifin wani da kuma yi da shi .

Manzon Allah (S.A.W .W )na cewa:

‘’ Mafi alkhairin mutane (mai dabara/wayo )shine wanda hangen laifukansa ya shagaltar da shi daga hangen laifin wani .‘’

Ma'ana, duk wanda a kullum ya kasance yana hangen laifukan kansa da gazawarsa , to, ba zai taba bude ido ya hangi laifi ko gazawar wani ba ballantana ya zama wata fitina gare shi.

Abinda ya fi alkhairi a rayuwarmu shine kowa yayi ta kansa, domin matuqar ka kyautata alaqarka da mahaliccinka, to, wanda ke kan bata ba zai bata cutar da kai da komai ba.

Allah mai girma da daukaka na cewa:

‘’ KUYI TA KANKU, WANDA YA BATA BA ZAI (iya )CUTAR DA KU (da wani abu )BA MATUQAR KUN SHIRYU (akan kanku ).‘’

         (QUR'AN )

Amma tambayar da ya kamata mu yiwa kanmu ita ce,

(ARE WE RIGHTLY GUIDED )?

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

        09039791509

~21st May, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post