Abin Koyi Mai Kyau Daga Rayuwar Kafirai!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

QALU-BALE GA AL'UMMAR MUSULMI

Matuqar magana ta Manzon Allah (S.A.W .W )ce ba za ka bata samun cin karo cikinta ba ballantana kuma maganar Allah. To, kamar yadda Allah (T )ya umarce mu kan cewa muyi koyi daga rayuwar Manzon Allah (S.A.W.W ), hakama yayi mana umarnin koyi da abu mai kyau daga rayuwar kafirai .

Rarrabar kai cikin al'umma ba boyayyen al'amari bane, domin Manzon Allah (S.A.W .W )ya sanar damu cikin wani hadisi da yake cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Lalle Yahudawa sun rabu gida 71, su ma Nasara sun rabu gida 72, kuma da sannu wannan al'umma za ta rabu gida 73, dukkansu (72)suna wuta, sai dai guda daya (1).‘’

Suka ce, su waye yaa Ma'aikin Allah ? yace;

‘’ WANDA NAKE KANSA DA SAHABBAINA .‘’

To, kowanne bangare daga cikin 73 dinnan suna da'awar sune akan daidai . Wannan shine tunanin 'yan 'Dariqa, Izala , JTI, Salafiyya , masu tunanin babu qunqiya muslimci kawai, da kuma 'yan Shi'ah.

        ABIN TAKAICI

Cikin da'awar da ke iqirarin cewa ita ce akan daidai sai ka samu babu fahintar juna, wadannan na sukar wadannan , tare da fatan aukuwar sharri ga bangare , tausayi da qaunar juna ta dade da ficewa daga cikin zukatansu.

Su kuwa kafirai babu wannan matsala tare da su duk da wannan rabe-rabe nasu. Shine Allah (T )ke umartar mu da cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ WADANDA SUKA KAFIRTA (kafirai )SASHEN SU MASOYI NE GA SASHE , IDAN (ku musulmi )BA KU AIKATA SHI (wannan soyayyar juna )BA , FITINTINU ZA SU KASANCE A BAN QASA DA FASADI MAI GIRMA !‘’

       (Anfal:73)

Wannan dai tunatarwa ce .

Daga wakilanmu na B auchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~20th may, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post