Idan Zuciyar Mutum Ta Ƙeƙashe Bata Ɗaukar Darasi!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Hankali da tunani shine babban abinda ke bambance tsakanin mutum da dabba , kuma shine ke fassara shi wanene cikin mutane. Idan aka rasa hankali da tunani tare da mutum yakan zama tamkar dabba, wani lokaci kuma dabba ma takan fi shi, domin takan iya gujewa abinda zai cutar da ita idan ta gan shi.

Qur'ani na dauke ne da gargadi, kwadaitarwa da kuma tarihi . Cikin wadannan abubuwa ukun ne me hankali da tunani ke wa'azantuwa .

Za kaga abubuwa na aukuwa ga mutum ko kuma cikin qasa don a dau darasi , amma masu qeqasasshiyar zuciya ba sa daukar darasi .

Allah (T )ya bamu labari da cewa:

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Kuma lalle mun aika (Manzanni )zuwa ga al'ummu daga gabaninka (don tsoratarwa amma suka kau da kai), sai muka kama su da tsanani (yunwa )da cuta (ta annoba ko jinyace-jinyace ), tsammaninsu za su qanqan da kai (ga Ubangijinsu ).

To, don me, a lokacin da tsananinmu ya je musu ba suyi tawali'u ba? Sai dai kawai zukatansu suka qeqashe, kuma shaidan ya qawata musu abinda suka kasance suna aikatawa .

Sa'an nan kuma a lokacin da suka manta da abinda aka tunatar da su da shi (ta hanyar kawar da kai da yin watsi da shi ), sai muka bude a kansu qofofin dukkan komai (na daga mulki, dukiya da lafiya ), har a lokacin da suka yi farin ciki da abinda aka ba su (bisa tunanin cewa dabara ko tsoronsu ne ya sa aka ba su ), sai muka kama su kwatsam (ba tare da sun shirya ba), sai ga su sunyi tsuru-tsuru (da idanuwansu ).‘’

    (AN'AM, AYA TA 42-44)

To, masu irin wadannan zukata sun yi yawa a wannan qasa , shi yasa kullum ake qara fadawa cikin qunci .

Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;

‘’ Idan kaga Allah na bada wani abu ga bawa a duniya alhali yana saba masa, to, ba sonsa yake ba, a'a, hakan shigo-shigo ne .‘’

      (Musna Ahmad, J:4, SH:145)

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~21st May, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post