Sahabbai Sunyi Ridda Bayan Wafatin Annabi Muhammad (s.a.w.w) – Inji Bukhari Da Muslim







IDAN DUK ABINDA KE CIKIN BUKHARI DA MUSLIM YA INGANTA; KENAN SAHABBAI DA YAWA 'YAN WATA NE?

Bukhari da Muslim sun tabbatar da cewa; Sahabbai sun yi ridda bayan wafatin Annabi(saw).

Bukhari da Muslim sun ruwaito cewa;

"... Ibn Abbas(r) ya ce wata rana Annabi(saw) ya yi khuduba yana mai ce: ...za'a zo da wasu mazaje daga Al'ummata, sai a yi wuta da su, sai in ce ya Allah! ai wadannan Sahabbaina ne fa! sai a ce da ni ai ba ka san abin da suka aikata ba; sun yi ridda bayan wafatinka..."

Ga nassin hadisin kamar yanda yazo a Bukhari:

4740 حَدَّثَنَا سُلَيْمَانُ بْنُ حَرْبٍ، حَدَّثَنَا شُعْبَةُ، عَنِ الْمُغِيرَةِ بْنِ النُّعْمَانِ - شَيْخٌ مِنَ النَّخَعِ - عَنْ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ، عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ(رَ) قَالَ: خَطَبَ النَّبِيُّ(ص)... أَلَا إِنَّهُ يُجَاءُ بِرِجَالٍ مِنْ أُمَّتِي، فَيُؤْخَذُ بِهِمْ ذَاتَ الشِّمَالِ، فَأَقُولُ : يَا رَبِّ أَصْحَابِي. فَيُقَالُ : لَا تَدْرِي مَا أَحْدَثُوا بَعْدَكَ. فَأَقُولُ كَمَا قَالَ الْعَبْدُ الصَّالِحُ : { وَكُنْتُ عَلَيْهِمْ شَهِيدًا مَا دُمْتُ }، إِلَى قَوْلِهِ : { شَهِيدٌ }. فَيُقَالُ : إِنَّ هَؤُلَاءِ لَمْ يَزَالُوا مُرْتَدِّينَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ مُنْذُ فَارَقْتَهُمْ".

- صحيح البخاري : كتاب التفسير. | سورة الأنبياء. | باب : كما بدأنا أول خلق : 4740 ( 3349, 3447, 4625, 4626, 6524, 6525, 6526, 6583 )

- صحيح مسلم ( 2860 )

- سنن الترمذي ( 2423, 3167, 3332 )

- سنن النسائي ( 2081, 2082, 2087 ).

- سنن الدارمي ( 2844 ).

- مسند أحمد ( 1913, 1950, 2027, 2096, 2281, 2327 )

Hadisin Haud (حديث الحوض) hadisi ne da ya tabbatar da akwai Sahabban da suka yi ridda bayan wafatin Annabi(saw) kuma zasu shiga wuta. Hadisin ya zo ta isnadai da sigogi da dama. Ga ruwayar Muslim:

6586 حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ صَالِحٍ ، حَدَّثَنَا ابْنُ وَهْبٍ ، قَالَ : أَخْبَرَنِي يُونُسُ ، عَنِ ابْنِ شِهَابٍ ، عَنِ ابْنِ الْمُسَيَّبِ أَنَّهُ كَانَ يُحَدِّثُ عَنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ(ص) أَنَّ النَّبِيَّ(صَ) قَالَ : "يَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ رِجَالٌ مِنْ أَصْحَابِي، فَيُحَلَّئُونَ عَنْهُ، فَأَقُولُ : يَا رَبِّ، أَصْحَابِي. فَيَقُولُ : إِنَّكَ لَا عِلْمَ لَكَ بِمَا أَحْدَثُوا بَعْدَكَ، إِنَّهُمُ ارْتَدُّوا عَلَى أَدْبَارِهِمُ الْقَهْقَرَى "....

- صحيح البخاري : كتاب : الرقاق | باب : في الحوض. ( 2367, 6583, 6587 )

- صحيح مسلم ( 246, 247, 249, 2302 )

- سنن ابن ماجه ( 4306 )

- موطأ مالك ( 64 )

- مسند أحمد ( 7968, 7993, 9292, 9856, 10030 ).

Bukhari da Muslim sun tabbatar da cewa; Annabi(saw) ya nuna zai yiwu wani wanda ba Sahabi ba ya fi Sahabbai imani da daraja a wajen Allah a ranar Qiyama.

"Abu Huraira ya ce; wata rana Annabi(saw) ya ziyarci Makabarta, sai ya ce; amincin Allah ya tabbata gareku ya ku Muminai ma'abuta wannan gida, inama a ce kun hadu da 'yan Uwana, sai Sahabbai suka ce; ai mu ne 'yan uwanka ko ya Manzon Allah(saw)? Sai Annabi(saw) ya ce; a'a, ku Sahabbai na ne, 'yan uwana su ne wadanda zasu zo bayanku, sai Sahabbai suka ce da Annabi(saw); ta ya zaka gane wadanda zasu zo bayanka daga al-ummarka? Sai Annabi(saw) ya ce; idan mutum yana da lafiyayyan rakumi mai haske, sai ya bata cikin rakuma marasa haske da lafiyya; ba zai gane nasa ba?.... za'a zo da wasu Sahabbaina (a ranar Qiyama a yi wuta da su)... Sai ace ai son canza (ridda) bayan ka yi wafati, sai in ce, ku yi wuta da su".

Ga nassin hadisin kamar yanda Bukhari da Muslim suka ruwaito:

4306 حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ بَشَّارٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ جَعْفَرٍ ، قَالَ : حَدَّثَنَا شُعْبَةُ ، عَنِ الْعَلَاءِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ ، عَنْ أَبِيهِ ، عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، عَنِ النَّبِيِّ(صَ) أَنَّهُ أَتَى الْمَقْبَرَةَ، فَسَلَّمَ عَلَى الْمَقْبَرَةِ، فَقَالَ : "السَّلَامُ عَلَيْكُمْ دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ، وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اللَّهُ تَعَالَى بِكُمْ لَاحِقُونَ "، ثُمَّ قَالَ : " لَوَدِدْنَا أَنَّا قَدْ رَأَيْنَا إِخْوَانَنَا ". قَالُوا : يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَوَلَسْنَا إِخْوَانَكَ ؟ قَالَ: " أَنْتُمْ أَصْحَابِي، وَإِخْوَانِي الَّذِينَ يَأْتُونَ مِنْ بَعْدِي، وَأَنَا فَرَطُكُمْ عَلَى الْحَوْضِ ". قَالُوا : يَا رَسُولَ اللَّهِ، كَيْفَ تَعْرِفُ مَنْ لَمْ يَأْتِ مِنْ أُمَّتِكَ ؟ قَالَ : " أَرَأَيْتُمْ لَوْ أَنَّ رَجُلًا لَهُ خَيْلٌ غُرٌّ مُحَجَّلَةٌ بَيْنَ ظَهْرَانَيْ خَيْلٍ دُهْمٍ بُهْمٍ، أَلَمْ يَكُنْ يَعْرِفُهَا ؟ ". قَالُوا : بَلَى. قَالَ : " فَإِنَّهُمْ يَأْتُونَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ غُرًّا مُحَجَّلِينَ مِنْ أَثَرِ الْوُضُوءِ ". قَالَ : "أَنَا فَرَطُكُمْ عَلَى الْحَوْضِ". ثُمَّ قَالَ : " لَيُذَادَنَّ رِجَالٌ عَنْ حَوْضِي كَمَا يُذَادُ الْبَعِيرُ الضَّالُّ، فَأُنَادِيهِمْ : أَلَا هَلُمُّوا . فَيُقَالُ : إِنَّهُمْ قَدْ بَدَّلُوا بَعْدَكَ، وَلَمْ يَزَالُوا يَرْجِعُونَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ. فَأَقُولُ : أَلَا سُحْقًا سُحْقًا ". 

- سنن ابن ماجه : كتاب الزهد | باب : ذكر الحوض 4306

- صحيح البخاري ( 136, 2367, 6583, 6586, 6587 )

- صحيح مسلم ( 246, 247, 249, 2302 )

- سنن أبي داود ( 3237 )

- سنن النسائي ( 150 )

- سنن ابن ماجه ( 4282 )

- موطأ مالك ( 64 )

- مسند أحمد ( 7968, 7993, 8413, 8741, 8878, 9195, 9292, 9856, 10030, 10778 ).

Haka zalika, Ummul-mu'umin Aisha ta ruwaito ingantaccen hadisi mai nuna Sahabbai da yawa zasu shiga wuta, ga nassin hadisin:

عَنْ عَائِشَةَ قَالَتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ(ص) يَقُولُ: (إِنِّي عَلَى الْحَوْضِ أَنْتَظِرُ مَنْ يَرِدُهُ عَلَيَّ مِنْكُمْ، فَلَيُقَطَّعَنَّ رِجَالٌ دُونِي، فَلَأَقُولَنَّ: يَا رَبِّ أُمَّتِي أُمَّتِي، فَلَيُقَالَنَّ لِي: إِنَّكَ لَا تَدْرِي مَا عَمِلُوا بَعْدَكَ، مَا زَالُوا يَرْجِعُونَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ).

- رواه أحمد (41 / 388) وصححه المحققون.

Sahabbai da yawa sun ruwaito Ingantattun hadisai masu nuna Sahabbai da yawa zasu shiga wuta, ga nassin kadan daga ciki:

6583 حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ أَبِي مَرْيَمَ ، حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ مُطَرِّفٍ ، حَدَّثَنِي أَبُو حَازِمٍ ، عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ قَالَ : قَالَ النَّبِيُّ(ص): "إِنِّي فَرَطُكُمْ عَلَى الْحَوْضِ، مَنْ مَرَّ عَلَيَّ شَرِبَ، وَمَنْ شَرِبَ لَمْ يَظْمَأْ أَبَدًا، لَيَرِدَنَّ عَلَيَّ أَقْوَامٌ أَعْرِفُهُمْ وَيَعْرِفُونِي، ثُمَّ يُحَالُ بَيْنِي وَبَيْنَهُمْ ".

6584 قَالَ أَبُو حَازِمٍ : فَسَمِعَنِي النُّعْمَانُ بْنُ أَبِي عَيَّاشٍ فَقَالَ : هَكَذَا سَمِعْتَ مِنْ سَهْلٍ ؟ فَقُلْتُ : نَعَمْ. فَقَالَ : أَشْهَدُ عَلَى أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ لَسَمِعْتُهُ وَهُوَ يَزِيدُ فِيهَا : " فَأَقُولُ : إِنَّهُمْ مِنِّي. فَيُقَالُ : إِنَّكَ لَا تَدْرِي مَا أَحْدَثُوا بَعْدَكَ. فَأَقُولُ : سُحْقًا سُحْقًا لِمَنْ غَيَّرَ بَعْدِي ". وَقَالَ ابْنُ عَبَّاسٍ : سُحْقًا : بُعْدًا. يُقَالُ : سَحِيقٌ : بَعِيدٌ، سَحَقَهُ وَأَسْحَقَهُ : أَبْعَدَهُ.

6585 وَقَالَ أَحْمَدُ بْنُ شَبِيبِ بْنِ سَعِيدٍ الْحَبَطِيُّ : حَدَّثَنَا أَبِي ، عَنْ يُونُسَ ، عَنِ ابْنِ شِهَابٍ ، عَنْ سَعِيدِ بْنِ الْمُسَيَّبِ ، عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ، أَنَّهُ كَانَ يُحَدِّثُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ(ص) قَالَ : " يَرِدُ عَلَيَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ رَهْطٌ مِنْ أَصْحَابِي، فَيُحَلَّئُونَ عَنِ الْحَوْضِ، فَأَقُولُ : يَا رَبِّ، أَصْحَابِي. فَيَقُولُ : إِنَّكَ لَا عِلْمَ لَكَ بِمَا أَحْدَثُوا بَعْدَكَ، إِنَّهُمُ ارْتَدُّوا عَلَى أَدْبَارِهِمُ الْقَهْقَرَى ".

- صحيح البخاري : كتاب : الرقاق | باب : في الحوض :
 ( 2367, 3349, 3447, 4625, 4626, 4740, 6526, 6586, 6587, 7050 )

- صحيح مسلم ( 246, 247, 249, 2290, 2302, 2860 )

- سنن الترمذي ( 3167 )

- سنن النسائي ( 150, 2087 )

- سنن ابن ماجه ( 4306 )

- موطأ مالك ( 64 ).

- مسند أحمد ( 2096, 2281, 2327, 7968, 7993, 9292, 9856, 10030, 11138, 11220, 11345, 11591, 22822, 22873 ).

Sahabi Abdullah Bin Mas'ud shima ya ruwaito ingantaccen hadisi mai nuna Sahabbai da yawa zasu shiga wuta, ga nassain hadisin:

عن عَبْد اللَّهِ بنِ مسعود قال: قَالَ النَّبِيُّ(ص)،(أَنَا فَرَطُكُمْ عَلَى الْحَوْضِ لَيُرْفَعَنَّ إِلَيَّ رِجَالٌ مِنْكُمْ حَتَّى إِذَا أَهْوَيْتُ لِأُنَاوِلَهُمْ اخْتُلِجُوا دُونِي، فَأَقُولُ: أَيْ رَبِّ أَصْحَابِي يَقُولُ: لَا تَدْرِي مَا أَحْدَثُوا بَعْدَكَ).

- رواه البخاري (6642) ومسلم (2297).

Sahabi Barra'u bin Azib ya tabbatar da Sahabbai da yawa sun yi ridda:

"ﺣﺪﺛﻨﻲ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺇﺷﻜﺎﺏ ﺣﺪﺛﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻓﻀﻴﻞ ﻋﻦ ﺍﻟﻌﻼﺀ ﺑﻦ ﺍﻟﻤﺴﻴﺐ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻗﺎﻝ ﻟﻘﻴﺖ ﺍﻟﺒﺮﺍﺀ ﺑﻦ ﻋﺎﺯﺏ ﻓﻘﻠﺖ ﻃﻮﺑﻰ ﻟﻚ ﺻﺤﺒﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ﺹ) ﻭﺑﺎﻳﻌﺘﻪ ﺗﺤﺖ ﺍﻟﺸﺠﺮﺓ ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎ ﺍﺑﻦ ﺃﺧﻲ ﺇﻧﻚ ﻻ ﺗﺪﺭﻱ ﻣﺎ ﺃﺣﺪﺛﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ.

"Al-Musayyib ya ce na hadu da Barra'u Bin Azib. Sai na ce; ku (Sahabbai) kun dace, kun zauna da Annabi(saw) kuma kun yi masa mubaya'a a karkashin bishiya. Sai Barra'u yayi ajiyar zuciya ya ce; ai baka san abinda muka yi ba a bayan (wafatin Annabi(saw) ba ne!"

(ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ، ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻤﻐﺎﺯﻱ، ﺑﺎﺏ ﻏﺰﻭﺓ ﺍﻟﺤﺪﻳﺒﻴﺔ)...

Ingantattun hadisai da suke tabbatar akwai Sahabban da zasu shiga wuta suna da yawan gaske a littattafan Ahlus-Sunnah, wadannan dan tsakure ne muka yi.

SHIN AKWAI ZAGIN SAHABBAI DA YA KAI A KIRASU 'YAN WUTA? KENAN AHLUS-SUNNAH SUN FI KOWA ZAGIN SAHABBAI TUNDA SUN INGANTA HADISAN DA KE KAFIRTA SAHABBAI?

IDAN DUK SAHABBAI 'YAN AL-JANNAH NE; ME YA SA BUKHARI, MUSLIM, AHMAD BIN HAMBAL... ZASU RUWAITO INGANTATTUN HADISAN DA KE TABBATAR DA AKWAI 'YAN WUTA CIKIN SAHABBAI?

IDAN HAR DUKKAN MALAMAN AHLUS-SUNNAH SUNA DA AKIDAR DUK SAHABBAI 'YAN AL-JANNAH NE; ME YA SA ZA'A SAMU INGANTATTUN HADISAN DA KE TABBATAR AKWAI 'YAN WUTA CIKIN SAHABBAI A LITTATTAFANSU?

KENAN YA ZAMA WAJIBI A FARA KAFIRTA DUK WANI MALAMIN AHLUS-SUNNAN DA YA RUWAITO INGANTACCEN HADISIN DA YA TABBATAR AKWAI 'YAN WUTA CIKIN SAHABBAI?

ME YA SA AHLUS-SUNNAH DA SU KE DA AKIDAR DUK SAHABBAI 'YAN AL-JANNAH NE; SU KE AMFANI DA SAHIHUL BUKHARI, MUSLIM, MUSNAD... ALHALI AKWAI HADISAI INGANTATTU CIKINSU DA SU KE TABBATAR AKWAI SAHABBAI 'YAN WUTAR JAHANNAMAH?

KENAN YA WAJABA AHLUS-SUNNAH SU WATSAR TARE DA KONA DUK WANI LITTAFIN HADISI DA KE DAUKE DA HADISAI INGANTATTUN DA KE TABBATAR DA AKWAI SAHABBAI 'YAN WUTAR JAHANNAMAH?

IDAN DUK SAHABBAI 'YAN AL-JANNAH NE; ME YA SA ALLAH ZAI SAUKAR DA SURAR MUNAFUKAI A QUR'ANI?

YA ZAMU YI DA AYOYIN DA KE TABBATAR DA AKWAI MUNAFUKAI CIKIN SAHABBAI?

KO MASU AKIDAR DUK SAHABBAI 'YAN AL-JANNAH SUN YARDA DA AKIDAR TAHRIFI (JIRKITA QUR'ANI TAHANYAR RAGI KO KARI)?

Saboda haka duk wanda ya ce kacokaf din Sahabbai yardaddun Allah ne, to ya karyata Al-Qur'ani da ingantattun hadisai. Haka ma duk wanda ya ce; kacokaf dinsu mutanen banza ne, shima ya karyata Al-Qur'ani da ingantattun hadisai.

➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com

🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post