Daga Shafin AL-IRSHAD FOUNDATION_*
Karkashin kulawar Hujjatul Islami Dr. Shu'aibu Muh'd
Ta binciko wa al'umma gwargwadon abinda za su fitar na zakkar fidda-kai
Domin saukaka masu da taimaka masu wajen sauke nauyin da shari'a ta dora masu.
Dama abinda kowane mutum zai fitar shi ne să'i daya, wanda ya yi daidai da kilogram uku, to shi wannan kilogram uku din shi ne ya yi daidai da gwangwani 18 na shinkafa, in kuma masara ce da yake ba ta kai nauyin shinkafa ba gwangwani 22 za ta kama.
1- Idan shinkafa mutum zai bada to zai bayar da gwangwanin madara goma sha takwas ne 18. (Wato kimanin kwanon shinkafa daya da gwangwani biyu kenan). Shi ne na kowane mutum daya.
2- Idan kuma masara mutum zai bada to zai ba da gwangwani ashirin da biyu ne 22. (Kimanin kwanon masara daya da gwangwani shida kenan) na kowane mitum daya.
Idan kuma mutum kimar kudin abincin zai bada, ba abincin ba, to sai ya bincika a inda yake ya gono kimar kudin adadin abinda aka fadi sai ya bayar.
MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
Tana yi maku fatan alheri da fatan Allah ya karbi ibadunmu.
Bin Haroun Sigau
21/5/2020.
Tags:
Ahkamul islam