@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DON RAININ WAYO AKA CE ABDULLAHI BN UBAIYI BN SALUL NE
Rashin adalci ne ka kasa ganin laifin wanda ya fadi magana ko ya rubutata cikin littafi, sannan kuma aga laifin wanda ya maimaita fadin abinda wasu suka riga shi fada.
Ba don ana so mu dau darasi cikin Qur'ani ko Hadisi ko littafan tarihi ba, da sai muce babu hikima cikin rubuta su, amma dai wannan shine tunanin wasu.
Ba soyayya bace kace za ka lullube laifin wanda kake so, sannan ba adalci bane dora laifi kan wanda bai aikata komai ba (innocent ).
Yana daga cikin babban makami da wasu ke dauka don yaqar 'yan shi'ah da sunan wai suna zagin sahabbai , alhali qarya ake yi musu , domin duk abinda ka ji sun fada yana nan rubuce cikin littattafai, sai dai kawai in karatunka ne bai kai kansa ba.
Rashin gata ce kawai tasa aka bayyanar da sunan ABDULLAHI BN UBAIYI BN SALUL cewa munafuki ne, amma su 12 ne fitattu in ji Annabi (S.A.W.W ).
Muslim ya riwaito daga Qatadata, daga baban Nadrata , daga Qais Bn Ubada , daga Ammar Bn Yasir yace, Huzaifata ya bani labari daga Annabi (S.A.W.W )yace;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Cikin Sahabbaina akwai munafukai 12, ba za su shiga Aljannah ba har sai Raqumi ya shige ta qofar allura (abinda ba zai taba yiwuwa ba kenan ), 8 daga cikinsu dabilata za ta isar ma a kansu , (dabilata )wata fitila ce daga wuta, za ta ratsa tsakanin kafadunsu (shoulders )har sai ta kama zukatansu .‘’
(Muslim, J:8, SH:123).
To, su waye ne wadannan munafukan?
Gaskiyar magana dai sune wadanda riqa cin dunduniyar Annabi (S.A.W.W ), kuma suka hanawa ruwa gudu bayan wafatinsa (S.A.W.W ).
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~31st May, 2020/ 10-10-1441.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
