MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SAHABBAI MA BASU TSIRA DAGA IRIN WANNAN TUNANI BA
Da shike al'amarin hukunta bawa ba a hannun wani yake ba yasa Allah ya boye al'amarin munafukan zamanin Annabi (S.A.W.W), sai dai kawai wadanda ya bayyanar masa dasu, amma suna nan birjik a tare da shi bai sansu ba.
Matuqar mutum ya furta kalmar shahada, to, kai baka isa fitar da shi daga da'irar muslimci ba ballantana zartar mar da hukunci kisa.
Amma wani abin mamaki shine sai ka ji wasu mutane na cewa wai 'yan Shi'ah kafirai alhali suna sane da cewa suna furta kalmar LA'ILAHA-ILLALLAHU MUHAMMADAR-RASULUL LAH, har ka ji suna halatta jinanansu bisa jahilci.
Ga wani hadisi inda Annabi (S.A.W.W)ke cewa Usama Bn Zaid yayin da ya daukaka akan wani mutum da Takobi sai yace; ‘’ LAA'ILAHA ILLALLAHU .‘’ Sai ya sare shi ya kashe shi. Sai aka ambatawa Manzon Allah (S.A.W.W)abinda ya faru, sai ya cewa Usamah ;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ KA KASHE SHI BAYAN YACE LAA'ILAHA ILLALLAHU .?YA ZA KA AIKATA DA WANNAN LAA'ILAHA ILLALLAHUNSA RANAR ALQIYAMA .?
Sai Usama yace, yaa Ma'aikin Allah, ai tafadeta ne dan neman tsari. Sai Annabi (S.A.W.W)yace;
‘’ ME YASA BA KA TSAGA ZUCIYARSA (ka tabbatar cewa da gaske ya fadeta)BA? Yana fada yana maimaitawa.
‘’ YA ZA KAYI DA LAA'ILAHA ILLALLAHUNSA RANAR ALQIYAMA .?
Usama yace, sai da nayi fatan ina ma ban muslimta ba sai wannan ranar (don ta kankare min zunubaina).‘’
- Muslim, J:1, SH:66
- Sunan Abu Dawud, J:3, SH:44
- Ibn Majah, J:2, SH:1396
- Musnad Ahmad, J:5, SH:207
TO, KAI MENENE MADOGARARKA A SHARIA NA HUKUNTA 'DAN SHI'AH A MATSAYIN KAFIRI DA HALATTA JININSA?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~6th May, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN