✍Aljawadu Shi'a kagara
_*SUNANSA:*_ Al-Hassan
_*LAKABINSA:*_ Al-Mujtaba
_*Al-KUNYA:*_ Abu Muhammad
_*MAHAIFINSA*_ Sayyidina Ali bn Abi Talib (AS)
_*MAHAIFIYARSA:*_ Sayyidatuna Fatima (AS) Diyar Manzo (S)
_*HAIHUWARSA*_ An haifeshi a madina ranar Talata, 15 ga Ramadan, shekara ta 3 bayan Hijira.
_*RASUWARSA*_ Ya rasu yana da shekaru 46, a madina ranar Alhamis 28 game safar An rufeshi a Baki'ah Imam Has an shine Babban Dan Imam Imam Ali da Fatima (AS) kuma jikan farko awajen Manson Allah (S.A.W.W) Tarihi yazo cewa loqacin da manzo (S) ya sami labarin haihuwar Imam hassan sai ya nufo gidan cikin gaggawa ya dauke shi ya karanta mass Koran sallah a kunnensa na dama, ikama a kunnensa na hagu, ya kuma sanya masa suna Al-hassan.
Ya tashi abisa kulawa ta manzo Allah (S.A.W) Ubangiji ya hore masa Ilimomi akan Fannoni daban-Daban ga hikima da hangen nesa. Kai hatta wani abin dake rubuce a lauhul-mahfuz Ubangiji yayi masa baiwar sanin sa.
Tarihi yazo cewa Imam hassan yasha fadawa mahaifiyarsa Fatima wata Aya data sauka tun kafin manzo (S) ya shaida mata.
Imam Hassan yana da Ibadar gaske yadda ta kai daga ya fara Alwala fuskansa takan canza domin tuna Allah. Ya kan jima yana sujadah. Gashi kuma da zurfin tafakkuri na Allah.
A zamaninsa babu Wanda ya taba kama da manzo (S.A.W) kamar sa. Yana da qaunar fakirai game kuma kyauta Yakan saka sharri da Alkairy An yi zamanin da za,a zo a zageshi a zagi babansa amma sai ya dauki kyautar kudi ya bayar ga mai zagin.
Yana da hikimar magana wadda takai maqiyansa na tsoron fuskantarsa da baki. Gashi kuma jarumin gaske be Wanda ya Sha daga mahaifiyarsa ya kuma tarbiyyantu daga bananas.
Imam hassan shine Wanda Imam Ali (AS) ya tura tare da kanensa hussaini domin su kare khalifa Usman, lokacin da daular musulmi shiga rudu , Wanda har wasu na kira da a kashe Usman din.
Sayyidina Ali ya kan dubi sauran 'ya'yansa yace masu "kune 'yayana amma hassan da hussaini 'yayan Annabi (S.A.W) ne"
_*KHALIFANCINSA*_
Bayan imam Ali yayi shahada sai musulmai suka za6i Imam hassan daya zama khalifansa, wanda kuma ya kar6a harya fara tafiyar da al'amuran mulki. Amma kwatsam sai Mu'awiyya yayi masa Tawaye ya kuma turo masa runduna don ta yake shi. Dams Manzo (S.A.W) ya fada cewa haka din zata faru.
Imam hassan yayi niyyar ya fuskance shi a gwabza amma sai mu'awiyya yayi amfani da yaudara da "siyasa" wajen kawo rudu acikin kwamandojin Imam hassan din. Daga karshe dai Imam hassan ya yarda zaibar mulki ga mu'awiyya amma bisa wasu yarjejeniyoyi, kamar haka:
1.Mu'awiyya zaiyi hukunci da Al-kur'ani da sunnar manzo da ta khalifofi salihai.
2.Ba zai Alqawarta wani amatsayin magajinsa b.
3.Mabiya Imam Ali zasu amintu daga duk wata fargaba.
4.Za a daina zagin Imam Ali a mimbirori da kuma cikin qunuti da hudubobi.
Mu'awiyya ya yarda da duk wadannan ka'idoji kuma akan haka Imam hassan ya ajiye duk wani sha'ani na mulki a hannun mu'awiyya shi kuma ya shagaltu da Ibadah da karantarwa.
_*SHAHADARSA*_
Tarihi ya tabbatar cewa guba aka bashi ya sha. Matarsa ja'adah diyar Ash'ath tayi ikirarin cewa an hada kai da itane aka bata guda domin ta sanyawa shi Imam hassan a cikin abinci Kuma akayi mata Alqawarin za,a daura mata Aure da Yazeed Dan mu'awiyya a Kuma bata dirhami dubu hamsin. Ta cika Aikinta amma ita Kuma ba'a cika mata Alqawarin ba.
Bayan rasuwar Imam hassan ne sai mu'awiyya ya Nada dansa Yazeed amatsayin khalifah, sa6anin yarjejeniyar da akayi dashi.
Imam hassan yayi shahada yabar 'Yaya ashirin da biyu goma share Biyar maza, sauran kuma mata.
Tags:
Munasabobi