CUTAR CORONA A QASASHENMU


~ Aɗɗalib Ahmad Harun
Wato yadda na lura da batun Coronavirus 'din Qasashen nan namu ta yanayin matakan daqile cutar shine,a na yin na Taguwar Annabi Salihu ne,kamar yadda Allah yake bamu labari a harshen Annabin zamanin,"...Wannan raquma ce tana da sha na yini,Kuma kuna da shan (Wani) yinin sananne",(Shu'ara).
Cutar na da wasu ranaku,suma mutane na da ranakun fitowa harkokinsu.Eh,mana,to ranar da mutane za su fito ba za ka ji wani ya kamu da ita ba,hasalima hatta jami'an tsaron da ke kula da shige da ficen jama'ar za ka gansu ba ababen kariya daga cutar,duk da ko yamutsi;Turnuquqi;Cunkoso da kusansar juna da ake samu mai yawa.
Wasu guraren ka ga amba Coronar kusan duk satin,sai aba mutane wasu 'yan ranaku,a wani gurin kuma a ba mutane yini,ita kuwa Coronar a bata dare (Sai ta fito tai ta walawa!).
Kamar A jahar Kano an ba Coronar kwana 5,mutane kuma kwana biyu.A yayin da a Kaduna kuma Kwana 'daya a ka ba mutane cikin sati (Duk sauran ranakun na Corona ne!).Ita kuma jahar Niger baya ga kwana biyu da aka ba mutane,an ba Musulmai awa 'daya dan sallar Juma'a a ranar Juma'a.Suma Kiristoci haka a ranar Lahadi.
A ya yin da kuma a Yamai Babbar birnin Jamhuriyyar Niger  Yini a ka ba mutane,ita kuma Coronar aka bata dare.To amma nai mamaki da ta yadda,duba da yadda ta saba da kaso mai tsoka (Ko ko an bata cin hanci ne!).
Ba fa ina kore cutar bane 'Absolutely' ,ba kuma ina nufin Hukumomi su garqame mutane 'Totally' a gida ba.Sannan ba sa mutane su daina amfani da hanyoyin kare kai nake ba,No,kawai dai 'dan tsokaci ne nai dangane da yanayin da na ga Cutar a Qasashenmu.Yanayi ne zai bai bayar da yin komai ,koda ko garqame mutane ne a gida,kamar yadda muke gani a Qasashen da Cutar tai qamari,irin su Iran,Italiya,Faransa,Amurka da sauransu.
*{Fa'atabiruu ya ulil-albaab}.
*"Ma aksarar Ibar wa aqallal I'itibaar".
*Wama uutiitu minal Ilmi illa qaliilaa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post