Shawarar sheikh yakubu yahaya katsina:- Alarammomi kuma ku nuna kune tunda anzo wajen







..Shawarwarin Shaikh Yakub Yahya Katsina kenan garesu, kan makircin azzalumai na kokarin rufe makarantun Allo da fakewa da Kurona, ci gaban jawabinsa ne bayan gama tafseer a jiya Litinin 19/10/1441. Asha karatu lafiya..._
"Ga kuma Makarantun Allo, kaga su Nijar ai basu watsa makarantun Allo ba, basu ci mutuncin Alkur'ani ba. Taba almajiri 'Danger' ce, (hatsari ne) saboda da shi da wanda ya tafi makka wanda ake ce ma Dhuyufur Rahman (baqin Allah), mahajjaci bakon Allah ne haka Almajiri wanda yayi hijira dan ya samu yardar Allah, ya samu addinin Allah shi ne Muhajiri (ai daga Muhajiri ne aka samu Almajiri) to shi bai zo wajen kowwa ba wajen Allah ya taho...taba shi kuma fada da Allah ne. Idan ana ganin akwai matsaloli to a gyara matsalolin, idan ana ganin sun kasa a tallafi kasawar su, shin karatun nan nasu yanada amfani ko bai da amfani? Yana da amfani, yana matsaloli? eh! To a gyara matsalolin a bar amfanin ne, amma ba ace a rusa baki daya ba. Kuma sannan a bar Boko.
Naji Shaikh Dr. Halliru Maraya yana magana yana cewa; duka-duka karatun bokon nan yau shekara 170 da fara shi amma karatun allo (na Alkur'ani) yau shekara 800 da wani abu ana yi shi, to yaushe ne bako zai kori dan gida?. To muna ganin kamar kuronan Najeriya ya ban-banta kawai ana ma wasu hidima ne. Alal misali akwai wani 'Senior Nurse' ne yace mani; an zaunar dashi gida an ce masa ya bar zuwa asibiti, wai a lokacin da ake bukatan zuwa asibitin aka ce masa wai bar zuwa akwai ma wata 'encharge' ce ita ma ance mata ta zauna gida. Akwai ma nan wani Program na BBC da suke yi ranar Asabar da safe kila wasu sun ji shi, ya suke ce mashi (Gane man hanya). Wata mata tace 'yar'uwar ta a kano tun karfe 2 dare ta ke cewa; azo a taimaka mata nunfashinta zai dauke sai suka ce mata "sai 8 na safe likita zai zo". Tace "yanzu ba mai taimakona kuna nan zaune zan mutu?..." Tana ta dai irin wadannan maganganun. Matar tace da ta matsa masu sai suka ce mata "ke baiwar Allah kije ki hakura daga sama an ce mana kar mu kara taba marasa lafiya". Shin ba manufa cin wannan abun?
Shin yanzu babu wadanda suka gama makaranta suna nan a zaune basu da aikin yi? Ba likito da wanda sukayi ritaya da wadanda basu samu aikin yi ba? Yanzu ya kamata wannan tallafin a dauki marasa lafiya a basu trainin ko na sati 1 a bazasu cikin Al'umma suyi maganin wannan al'amarin, amma sai wanda ke ciki ake janyewa, shin mi wannan ke nufi? Kawai wata siyasa ce wata dama ce dama bayahude ko bai kirkiro abu ba yakan amfani da wata dama in yaga kafa to zai shiga su biya bukatar su.
Makarantun Allo duk an watsa ana nema a haramta ma, ina ganin daga wannan karon ma dai makarantun Allo sai abinda hali yayi amma dai zan yi kira ga su Malaman Allo alarammomin nan, tunda Allah ya kawo mu wurin to kuma ku nuna kune ku dukufa ku raba Alkur'ani ayi safka miliyoyi a hada ayi karo karo a samu raguna a yanka ai sadaka ko a sayi abinci a ba mutane ayi addu'ar Allah ya kawo karshen wadannan azzaluman. Kuna da makami a hannun ku kuna tare da Allah, Malaman Allo da Malaman Alarammomi su taru suyi karatun Alkur'ani... Ba sai na gaya masu ga abinda ya kamata suyi ba, su koma gurin Allah ba roko ya kamata zasuyi na abar su ba, su gaya ma Allah a barsu ko dan dole... Ba 'yar murya zasuyi ba, a saurara masu ko a tausaya masu... Wannan lokacinsa ya wuce ku dakko Alkur'ani kuyi alwala ku gaya ma Allah kuma ku hada kanku lokacin hadin kai ne yanzu... Madamar basu bari ba kuma kar ku bari shege ka fasa, matsiyata kawai.
Allah ya kawo karshen su wannan makirci ko wa ya kulla ko wa ya shirya Allah ya ruguza shi, Allah ya kawo karshan sa. Ance sun zo nan sun doki mutane asibiti hada ma likitan ma suka buga da marasa lafiya a can 'Medical Center' kuma iyalina Sunje damo ma yaro irin maganin nan da ake damo masa, jami'an tsaro sun cika wajan, motocin sojoji an kai asibiti an tsattsare. Bamu san mi suke nufi ba wallahi kuma gashi ana ta kashe mutane nan bakiyawa nan kasa da k/m 20 zuwa nan Katsina ana ta kashe mutane ana kwasar dabbobi, noma ma baya yiwuwa sam bana ba wanda zai je ma yayi kasadan fara noma, me ake nufi ne? Me ake so ayi ina mutane zasu shiga? To 'any way' suna tunkuda mutane ne zuwa neman mafita, suna sa mutane ne kan hanyar neman mafita. Eh! mana suna dora mutane kan hanyar neman mafita, kasan takarda in ta yage ko an sa sa gam an like sunan ta mene?... Idan haiba ta fadi... Ba'a bari a kwashe lafiya, mutuncinsu ya zube kuma daga nan za a dora ne nan gaba kadan za ka ji abinda zai biyo.
__Allah ya taimake mu Allah ya tsare bayinsa, Alah ka raya zukatan Muminai ka dawo damu cikin hayyacinmu ba dan halinmu ba, ka canza mana wannan mawuyacin halin zuwa kyakkyawan halin da ka fi so ka yarda da shi, Allah ta'ala ka yafe mana kura-kuran mu da laifukan mu, Allah mun gasu haka nan ka kawo mana dauki_ .
RABBANA TAQABBALMINNA INNAKA ANTAS SAMI'UN ALIM, WA TUB ALAINA INNAKA ANTA TAWWABUR RAHEEM.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post