Dukiyar Haram Bata Amfanar Da Ma'abocin Ta Da Komai!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DUK WANDA KAGA YANA RIQO DA ADDINI, TO, ALLAH YANA SONSA

Ni'imomin Allah ga dan adam na da yawa yadda baki ba zai iya lissafo shi ba, domin wasu ni'imomin a gangar jiki suke , wasu kuma abu ne a bayyane wadanda ake ganin gurbin su.

Cikin dukkan ni'imomin Allah ga bawa babu kamar ta addini , domin ita ce take amfanar da mai ita a duniya da lahira.

Dukkan wata ni'ima da bawa zai samu a duniya matuqar ba ta addini bace, to, takan zama hasara ce ko marar amfani gare shi a lahira, ko da kuwa yana ga kamar ya ji dadinta a duniya .

Abdullahi Bn Mas'ud ya bada labari daga Annabi (S.A.W.W )cewa yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Lalle Allah ya raba dabi'unku a tsakaninku (munana da kyawawa )kamar yadda ya raba arziqi a tsakaninku (wani talaka wani mai dukiya ).

Kuma lalle Allah yana bayar da duniya ga wanda yake so da ma wanda ba ya so, amma ba ya bayar da addini sai ga wanda yake so, duk wanda Allah ya ba shi addini to, yana sonsa.

Na rantse da wanda raina ke hannunsa, bawa ba zai taba zama musulmi ba har sai zuciyarsa da harshen sa sun kubuta(daga qulla sharri da cutar da mutane ), kuma ba zai taba zama mai imani ba har sai maqwabcinsa (his neighbour )ya aminta da bawa'iq nasa.‘’

Muka ce, menene bawa'iq nasa yaa Ma'aikin Allah ? Yace;

‘’ Qulla sharrinsa da zaluncinsa, kuma bawa ba zai tara dukiyar haram sannan ya ciyar daga gare ta kuma ya samu albarka cikinta ba, kuma ba zai yi sadaqa a karba masa ba, kuma ba zai barta (dukiyar )a bayansa ba face ta zama qari gare shi zuwa wuta . Lalle Allah ba ya shafe mummuna da mummuna, sai dai yana shafe mummuna da mummuna. Lalle mummuna ba ya shafe mummuna .‘’

(Musnad Ahmad , J:1, SH:387)

Daga wakilanmu ba Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

     09039791509

~27th May, 2020/ 6-10-1441.

karanta wasu LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post