Bello Yabo: Shin Mene Ne Laifin Zakzaky???





Zuwa yanzu an dumfari shekaru biyar ke nan da kama Sheikh Ibrahim Ya'aqub Zakzaky, amma har yanzu an kasa tabbatar da laifin da ya sa aka yi masa wannan kamu, kuma an qi sakinsa.

Da farko dai an nuna kamar da gwamnatin tarayya yake da case, aka dau lokaci bayan kama shi a ranar 14 ga watan Disamba 2015, ba a gurfanar da shi a kotu ba har aka shafe tsawon watanni, ya gaji da jiran gawon shanu ya maka gwamnatin a wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. A watan Disamba 2016 kotun ta ce a saki Sheikh Zakzaky cikin kwanaki 45 kuma a biya su diyyar wannan kamu da aka yi masa har na miliyan 50 shi da matarsa.

Gwamnati ba ta biya diyyar ba kuma ba ta sake shi din ba har na tsawon shekaru biyu. A tsakanin wannan lokaci sai jami'anta suka yi ta bayar da mabambantan ra'ayoyi kan dalilin kama shi, da dalilin cigaba da riqe shi, da kuma dalilin qin bin umurnin kotun da ta ce a biya shi diyya a sake shi. Dukkan dalilan dai babu na kamawa ga mai hankali.

Na biyu, wala'alla bayan ganin qorafe-qorafe a kan abin da aka yi wa Sheikh Zakzakin sun yi yawa ne, sai kwatsam aka ce gwamnatin Jihar Kaduna qarqashin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa'i, ta karbi case din, ta kuma gurfanar da Sheikh Zakzaky a wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a watan Afrilu, 2018, bisa zarginsa da aikata laifuka takwas, babban cikinsu shi ne kisan da aka yi wa wani soja a lokacin tashin hankalin kama shi.

Manazartan gida da wajen Nijeriya sun cika da mamakin dalilin wannan qara a wancan lokaci, saboda sojoji sun kashe 'yan qungiyar Sheikh Zakzaky, IMN, aqalla mutum 347 yayin wannan tashin hankali na kama shi, aka kuma turbude dukkan wadanda aka kashen a rami guda cikin talatainin dare, amma gwamnatin El-Rufa'i ba ta gurfanar da sojojin da suka yi wannan ta'annati kotu ba sai shi Zakzakin da matarsa da wasu mutane biyu cikin mabiyansa.

Lauyoyin Sheikh Zakzaky sun nemi a ba da belinsa, amma har zuwa yau an hana. Belin neman magani ma da qyar aka bayar shi ma cikin takurar da ta sa Shehin malamin ya haqura. Zaman shari'a kuma ana ci gaba da yi har yanzu.

Kwatsam! Sai ga Sheikh Bello Yabo na Sokoto, an ce ya zagi Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufa'i. Aka kama shi. Cikin kwana uku Ministan Shari'a da Ministan Sadarwa da wasu manyan jami'an gwamnati suka sa aka sako shi a ranar da ake hutun aiki.

Na'am, wani zai iya cewa ai laifinsu ba daya ba ne, haka ne. Amma shin don Allah wai mene ne haqiqanin laifin Sheikh Zakzaky da ya sa ake masa duk wadannan abubuwan kuma aka hana hatta belinsa?

Muhammad Bin Ibrahim
26/05/2020  karanta wasu LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post