@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ADDU'AR ALKHAIRI AKE YI A KANTA
Babu wanda ya san haqiqanin abinda zai tarar a lahira, amma sai ka ji jama'a na yiwa mutum fatan mutuwa saboda ganin tsananin jinyar da yake yi.
Annabi Ayuba (A.S )ya fada cikin matsananciyar jarrabawa ta jinya tare da yaqinin abinda zai tarar na alkhairi a lahira , amma duk da haka bai yi fatan mutuwa ba .
Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ KADA 'DAYANKU YAYI BURIN MUTUWA SABODA JINYAR DA TA SAUKA A KANSA , IDAN MAI KYAWAWAN AIKI NE AKWAI YIWUWAR SU QARU , IDAN KUMA MAI AIKATA MUMMUNAN AIKI NE WATAQILA YA TUBA.
SAI DAI (dayanku yace )YAA ALLAH !KA RAYAR DANI MATUQAR DAI RAYUWAR ALKHAIRI CE GARE NI, KUMA KA KARBI RAINA IN DAI MUTUWAR CE MAFI ALKHAIRI GARE NI.‘’
(Musnad Ahmad , J:3, SH:101).
Domin ya tabbata cikin wani hadisi da yake cewa, idan mutum ya kasance mai aikata wasu ayyukan alkhairi a halin lafiyarsa, to, ko da ya fada cikin rashin lafiya wanda jinyar ta hana shi aikata wadannan ayyuka , to, ba za a yanke masa ladan ayyukan da yake yi a halin lafiyarsa ba.
Sannan kuma ita jinya kankarar zunubi ne, kenan duk wanda ke halin rashin lafiya yana samun kankarar zunubi matuqar dai mumini ne.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~27th May, 2020/ 6-10-1441.
Tags:
Tunatarwa