@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
JAMA'A SUNA TA GUNA-GUNI DA WANNAN DOKA
Yana daga cikin makami mafi hadari wanda miyagun maluma ke amfani da shi wajen yaqar dukkan wanda ke qorarin yin tawaye ga wani azzalumi wajen qin bin umarninsa.
Ayar Allah ce wacce ba ka isa musanta fassararta ta zahiri ba yayin da aka kafa maka hujja da ita don kautar da tunanin ka zuwa inda masu fassarar ke so ka je .
Wannan ayar ita ce inda Allah (T )ke cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! KUYI 'DA'A GA ALLAH DA MANZONSA DA KUMA MA'ABOTA AL'AMRA DAGA CIKINKU .‘’
Bisa dogaro da wannan aya nake ba ku haqurin yin juriya wajen qara yin azumi 1don ku cike 30 kamar yadda mai martaba ya bayyana .
Gidajen radio sun ruwaito cewa ingantacce jawabi ya fito daga bakin mai martaba cewa ba aga jinjirin watan Shawwal a yau juma'a ba, saboda haka gobe za ayi azumi , sai kuma ayi sallah ranar lahadi .
To, a matsayinka na wanda yayi imani cewa wannan shugaba wanda sabawa umarninsa ya zama laifi da abin aibantawa, to, wajibi ne ka bi shi, domin saba masa tamkar warware bai'arsa ce da ke wuyanka .
Ai dama tun farkon azuminku kunyi niyyar azumtar kwana 29 ne ko 30 kamar yadda naji wani limami ke kafa muku hujja don ku kasance masu biyayya , kuma maganarsa haka ne, domin tunda ba ganin watan da idanuwanku ku kayi ba yayi dauka, yanzu ma ba ku gani ba dole ku bi don ba ku da hujjar bijirewa in dai ba so kuke ku zama 'yan tawaye kamar yadda kuke kiran 'yan shi'ah ba.
Na'am, wancan ayar ba za ta zama hujja ba a kanmu , domin mu mun san ba irinsu ne ULUL-AMRI da ake ce muyi musu biyayya ba, ku kuma kun yarda da haka har kuna aibanta mu.
In da ace irinsu ne ULUL-AMRI, to, da Allah bai umarci Musa (A.S )ya yiwa Fir'auna tawaye ba .
MUJE ZUWA, KOMAI NISAN JIFA QASA ZA TA FADO.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~22nd May, 2020.
Tags:
Ahkamul islam