@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DAMA ABIN NASU ISKANCI NE BA ADDINI BA
Yanzu ta bayyana cewa masu da'awar biyayya ga sarkin musulmi har suna kafirta wadanda suke da sabanin fahinta dasu, yanzu sun dawo sun zama daya wajen bijirewa umarnin wannan sarki ta hanyar qin cika azumi 30.
Ban san irin hujjar da za ku bayar ba kan wannan badaqalar da ake tafka ta cikin muslimci da sunan addini ba, kun ce biyayya gare shi wajibi ne amma yanzu kun zo kun warware wannan zance naku a aikace .
'Yan shi'ah sun sha ruwa jiya bisa dogaro da hujjar ganin wata kamar yadda fiyayyen halitta (S.A.W.W )ya koyar damu cikin addinin da yazo mana da shi, kan haka kuka ce dole sai sanarwar wata ya fito daga bakin sarkin musulmi kafin kuyi aiki da ita , alhali kaf cikin littafan addinin muslimci babu inda aka kawo haka ko da kuwa bisa tuntuben alqalami ne.
Yanzu sanarwar ta fito daga bakinsa amma kun qaryata shi, wanda hakan ke nuna cewa dama duk abinda kuke yi bin son zuciya ne ba addini ba, domin da addini dole ya kasance kun bi umarnin wannan shugaba tunda kuka ce biyayya gare shi wajibi .
SHEIKH SANI YAHYA JINGIR
A matsayinsa na babban malami mai da'awar kawar da bid'ah tare da tsayar da sunnah (ba dabbaqata ba ), ya fito ya yi kira ga mabiyansa kan cewa su cika azumi yau asabar ya zama 30.
Idan kun kasance masu biyayya ga shugabanni ya zama wajibi a kanku ku bi wannan umarni, domin rashin bin nasu zai canza su daga matsayin da suke zuwa wani matsayi na dabam.
Gaskiyar magana ita ce, matuqar ba ku bi umarnin wadannan shugabanni biyu saboda tunaninku kan cewa umarnin nasu ya sabawa dokar Allah , to, wajibin da ya hau kanku shine ku dawo daga rakiyar su ku riqi shugabanni na gaskiya masu biyayya ga Allah, domin haramun ne daukar wanda ba adali ba ya zama jagora a cikin addini ko ma wanne iri ne, domin halakakke ne mai halakarwa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah G uda.
09039791509
~23rd May, 2020/ 2-10-1441.
Tags:
Muhimman zantuka