Kaso Sittin (60%) Na Musulmi Mushrikai Ne!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

GASKIYA BA TA DA DADI, AMMA DOLE A FADE TA

Kada ka ji kalmar ta yi maka nawi ko girma ba tare da ka bibiyi wannan rubutu zuwa qarshensa a nutse ba, domin ba a yanke hukunci kan mutum ba tare da hujja ba.

Shan ruwan rubutu, daura laya ko guru ba shine shirka ba matuqar ka nemi yardar Allah cikinsu, domin duk daya suke da shan BOSKA ko PANADOL a babin magani.

Shirka ita ce hada Allah da wani cikin bauta ko kuma yin biyayya ga dokar wani wacce ta sabawa ta Allah . Matuqar mutum zai so ka aikata wani abu wanda Allah ya haramta ko ya hanaka aikata abinda Allah ya umarceka a kansa kuma kayi masa biyayya , to, kai mushiriki ne .

Allah (S.W.T )na cewa:

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Kuma lalle shaidanu suna yin ishara zuwa ga masoyansu (kan halatta jinanan 'yan'uwansu musulmi da bin dokar wanin Allah )domin suyi jayayya da ku (muminai kan kiran da kuke yi na a dawo kan bin dokar Allah ), kuma idan ku kayi musu biyayya lalle ku mushirikai ne.‘’

       (AN'AM, AYA TA 121)

Kuma yanzu halin da ake ciki kenan, shugabanni da malamai na halatta musu jinanan 'yan'uwansu da dukiyoyinsu , kuma suna yi musu biyayya kan haka.

Allah mai girma da daukaka ya qalubalanci Yahudu da Nasara cewa suna bautawa malamansu , inda yake cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Sun riqi Ahbar da Ruhban nasu abin bauta koma bayan Allah .‘’

Sai Adi Bn Hateem yace;‘’ Yaa Ma'aikin Allah, ba sa bauta musu fa !‘’ Sai yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Na'am, ai lalle suna halatta musu haram, kuma suna haramta musu halal , kuma suna bin su (kan wannan umarni ), to, ai wannan ita ce bautar tasu gare su .‘’

(Tuhfatul-Ahwaz na Tirmidhi, J:8, SH:492)

Ga shi kuma suna rahamta musu yin azumin ramadan a farkonsa, kuma suna halatta musu azumin ramadan a farkon Shawwal .

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

~22nd May, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post