An Bayyana Cewa: Jihadi Ne Kadai Hanyar Da Za A Iya “Yanto Da Palasdinu

Wani dan majalisar dokokin kasar Lebanon mai wakiltar kungiyar “Amal” Haj Muhammad Nasrallah ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Bayan gushewar shekaru 72 daga kafuwar HKI, yanzu tana fada da tarin matsaloli,don haka rushewarta wani abu ne da babu makawa.

(ROHOTON ABNA24.com) Wani dan majalisar dokokin kasar Lebanon mai wakiltar kungiyar “Amal” Haj Muhammad Nasrallah ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Bayan gushewar shekaru 72 daga kafuwar HKI, yanzu tana fada da tarin matsaloli,don haka rushewarta wani abu ne da babu makawa.

Haj Muhammad Nasrallah ya kara da cewa; Babu yadda za a yi ace wata bakuwar kasa da aka kafa ta a cikin wani yanki na al’ummar da ba nata ba, ta iya ci gaba da wanzuwa idan ba ta hanyar amfani da karfi ba da kuma samun taimako daga waje.

Dan majalisar na kasar Lebanon ya kara da cewa; Watakila daya daga cikin dalilan da su ka sa HKI ta ke ci gaba da wanzuwa shi ne raunin da larabawa su ke da shi saboda sun yi murabus daga taimakawa gwagwarmayar Palasdinawa.

Dan majalisar kasar ta Lebanon ya kuma yi ishara da yadda ake kara samun masu adawa da HKI, musamman kawancen masu gwagwarmaya da turjiya daga Tehran zuwa Palasdinu, da su ne za su ‘yanto da Palasdinu.


KU KARANTA WASU LABARAI ANAN;https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post