19TH RAMADAN, 40 (B.H), DARE DA AKA SARI IMAM ALI (A.S)!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MUTANE BIYU DA SUKA FI KOWA SHAQAAWA

Sakamakon yaqin siffin da akayi tsakanin Imam Ali (A.S)da Mu'awiyyah (L.A)wanda Amru Bn As da Abu Musa Al-Ash'ari su kayi wata yarjejeniya ta yaudara sai aka sami wasu mutane da ake kira Khawarij suka fandare daga rundunar Amirul Mumunina Imam Ali (A.S).

Wannan fandarewar tasu yasa suka ce ai jinin Imam Ali (A.S)dana Mu'awiyyah ya halatta, wanda hakan yayi sanadin yin yaqin NAHRAWAN. Bayan nasarar da Imam (A.S)ne ya samu a kansu sai suka tsara yadda za su kashe shi cikin ruwan sanyi.

Abdurrahman Ibn Muljam (L.A)ne ya dauki alqawarin sheqar da jinin Imam Ali (A.S), wanda yayi shiri zuwa kufah don aiwatar da wannan danyen aiki.

Bayan Imam Ali (A.S)yayi sahur sai ya nufi masallaci don gabatar da sallar asubahi, shi kuwa ibn Muljam (L.A) ya riga ya shiga masallaci dauke da Takobi mai guba yana jiran isowar Imam Ali (A.S).

Bayan Imam yayi kiran sallah ya wuce gaba yana jan sallah, da yayi sujadah sai Ibn Muljam (L.A) ya zaro Takobinsa mai guba ya sare shi (A.S)a tsakiyar kansa har jini ya jiqe gemunsa (A.S).

Wata rana Annabi (S.A.W.W)yake cewa Imam Ali (A.S);

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ BANA BAKA LABARI GAME DA MAFI SHAQAAWAR MUTANE BA?‘’

Yace, na'am yaa Ma'aikin Allah. Yace;

‘’ MUTANE BIYU NE, UHAIMARU BASAMUDEN NAN DA YA SOKE TAGUWA (Naaqata Salihu), DA KUMA WANDA ZAI SARE KA YAA ALIYU A WANNAN GURI (yana nufin tsakiyar kansa)HAR (jinin)YA JIQE WANNAN (yana nufin gemunsa).‘’

Wannan kuwa shine abinda ya faru gare shi a daren 19 ga Ramadan, shekara ta 40 bayan Hijrar Ma'aiki (S.A.W.W).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~10th May, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post