Alaƙar El-Rufa'i Da Shaiɗan





Daga Ma'asumah Nigerian News Update

Sanin kowane ma'abocin karatu ko sauraren tarihi ne cewa; babban abinda ya halakar da Shaidan shine girman kai. Jin cewa shi wani ne ya sanya yake kallon kansa a saman kowa, sabida haka shi ya cancanta ya kasance a birbishin kowa. Wannan dalilin ne ya halakar da Shaidan, duk matsayinsa dake wajan Allah ya zube, ya zama mafi kaskanci a cikin halittun Allah.

Ga duk wanda yasan halayyar El-Rufa'i a kujerar mulki, kuma yake nazari bisa halayyarsa, zai fahimci cewa babban abinda ke halakar da El-Rufa'i shine 'Girman Kai' Tabbas wannan dabi'a ta Shaidan itace tayi tasiri a rayuwar El-Rufa'i yake aikata duk iskancin daya so. Kasancewar yana ganin sa bisa wata kujera ta mulki, shiyasa yake jin cewa kamar kowama bawansa ne, sabida haka zai iya aikata komi ba tare da fuskantar kowace matsala ba, tunda shine a saman kowa.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Sayyid Zakzaky (H) Bai Ha'inci Ko Wa Ba
☞ ͡Subaykha Annubiyya Mahaifiyar Imam Jawad (A.S)
☞ ͡Wafatin Nana Khadijah, 10 Ga Ramadan
☞ ͡Bazan lamunta ba, Har Sai Naga Almajiri Na ƙarshe ya bar Plateau – Lalong

Tun daga farkon samun mukamin gwamnati da El-Rufa'i yayi, idan mu bibiyi salon da yake tafi da mulkinsa da yin nazari akai, zamu fahimci cewa tabbas El-Rufa'i yana jin kansa tamkar wani Allah ne, duk wadanda yake mulkansu su kuma tamkar bayinsa ne, shiyasa yake aikata duk abinda shaidaniyar zuciyarsa ta bujuro masa dashi. Da zamuyi la'akari da sauran masu mukaman gwamnati na yanzu, musamman gwamnoni sa'o'insa zamu ga cewa salon mulkin El-Rufa'i yasha bam-bam da nasu.

Kusan kowane gwamna idan zai zartar da doka a jaharsa yakanyi kokarin sassautawa koda kuwa zai zalumci yan jaharsa ne, amma shi El-Rufa'i duk dokar da zai zartar sai ya wuce gona da iri, kuma ko a jikinsa bai damu da halin da yan jaharsa zasu shiga ba. Ya maida takalawa tamkar ribatattun bayinsa wadanda zai iya sanya kafa ta taka, yaji kamar ya taka takalminsa. Wallahi wannan itace mafi munin dabi'ar da tayi tasiri ga El-Rufa'i kuma ta halakar dashi.

Sabida haka idan har El-Rufa'i bai canja ba, to lallai zai zama sakamakon sa iri daya ne dana maigidansa Shaidan, kuma makomarsu zai zama daya anan duniya da lahira. Babu makawa abinda zai faru kenan matukar bai canja ba.

– Abbakar Ibraheem Kudan.
   3/05/2020.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post