Covid-19 da gwamnatin Nijeriya – Nazari





Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Akwana kwanan'nan wani masani a ɓangaren lafiya kuma Shehin malami, Prof.Usman Yusuf tshohon shugaban hukumar Inshorar lafiya ta Nigeriya, yayi wata magana mai matuƙar tada hankali, amma ga mai hankalin.

Yace Nigeriya Idan ba'ayi taka tsantsan ba, sai takaiga mutane na faɗuwa suna mutuwa saboda cutar COVID-19. Ana cikin wan'nan jimami da sharhi akan maganar Prof. Sai ga wata ta fito tacika kafafen sadarwa na zamani, wato New media's cewa Shugaba Trump na Amurika yace Nigeriya saitafi ko wace ƙasa a duniya yawan masu kamuwa da wan'nan cuta ta COVID-19.

SUBHANALLAH! Idan har maganar Trump ta inganta yafaɗi haka, kenan maganar Prof.Usman da ta Trump sunzama tagwayen juna.

Bani da wata cikakkiyar masaniya akan wane fanni Shugaba Donal Trump ya karanta, sai dai nasan ba masanin lafiya bane. Amma me yiyuwa ya lura da yanayin Society na mutanan Nigeriya, kamar yanda Shima Prof.Usman ya ga haka kuma ya sanar, don haka a matsayin prof. Usman na masanin lafiya, ya fita haƙƙin Ilimi.

Ba ina so inyi ko inkafa hujja da Shugaba Trump bane, domin su waɗan nan ni a ƙashin kaina ina ɗaukar Amurika da Trump amatsayin maƙiyan ƙasar mu Nigeriya, don haka don sunyi wan'nan maganar, ta iya yiyuwa subi duk'hanyar da zasubi domin maganar ta su ta zama gaskiya.

Don haka Ni inaganin wan'nan maganar ta Trump yakamata ne Gwamnati da 'yan ƙasa, su sanya ido kuma suyi taka tsantsan, duk'da a ita Gwamnatin Nijeriya ta ɗauki Amurika a matsayin aminiya kuma abin ƙauna.

 Amma duk da haka ina kira ga Gwamnati tasanya ido ga ƙasashe masu shigo mata, mukuma 'yan ƙasa mu kare kanmu ta hanyar addu'a da bin shawarar likitoci masana.

To amma ba'anan gizo ke saƙaba, inda matsalar take shine Ita gwamnatin Nigeriya ita da yakamata tayi iya ƙoƙarin ta, bama tun yau ba tuntuni ta samar da yanayin kiwon lafiya mai kyau mai ingancin da su kansu zasu iya taƙama da haka kuma su bawa 'yan ƙasa cikakkiyar kulawa, sai yazama tayi sakaci, sakacin da su kansu mahukuntan ƙasar basu gamsu da yanayin kiwon lafiyar ƙasar ba, kuma sun kasa yin wani hoɓɓasa akan haka.

Shi yasa ma sai kaga shugaba ɗan siyasa ya ware miliyoyin kuɗi, kudin da inda ace zai koma ƙauyensu ya gina asibiti, zasu isa agina, harda kayan aiki masu inganci, dakuma kwararrin likitocin da shi kansa zai iya kwanciya aduba lafiyar sa anan.

Amma waɗan'nan kuɗin zai kwasa yaje wata asibiti akasashe ƙetare kan matsalar da idan kaine talaka kana kasuwa neman na tuwo ciwan zai sameka har ka warke baka sani ba, shikuwa yaje ya zuba su, yayi wata ɗaya yana kwance suna latsa jikin sa suna ƙara bashi lokacin, cin kuɗi, tunda sungano shi wawa ne.

Idan nace a Nigeriya bamu da kwararrun likitoci banma likitoci adalci ba, saboda munga yanda ƙasashen da suka san mahimmancin kwarewa
Likitocin namu suke kwashe su suna kaisu ƙasashe nasu suna basu al'bashi mai tsoka suna masu aiki.

Amma duk'ɗan Nigeriya yasan cewa ƙasar nan bata da kayan aiki, misalin ɗan mashin ɗina nasan inda ake masa juye'amma bani da sufanar da zata kwance shi balle inyi, duk'yanda na kware wajen iya kwance ƙusar sai dai in kaima mai kayan aiki ya kwance yayi mun.

Haka ƙasar mu take, kuma ba wai babu kuɗin siyan kayan aikin bane, a'a maƙetatan shuwagabanni garemu, waɗanda basa ƙaunar talakka, sunriga sun saida rayuwar talakan da suke mulka sun amshi kuɗin.

Idan ba haka ba Nigeriya itace ƙasa mafi girma a Afrika, itace ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Afrika, san'nan kuma itace ƙasa mafi tsananin talauci, to ina wan'nan arziƙin yake shigewa? Amsa: aljihun ɓarayi 'yan siyasa.

Idan muka dawo akan maganar Prof. Usman yusuf kuma, wallahi ba, baki bane yake mana kuma ba muguwar fata bace, a'a a fahimtata ya duba yanayin abu biyu, Nafarko sakacin Gwamnatin akan kiwon lafiya, Nabiyu sakacin shi talakkan da ake mulka. Sakacin Gwamnati shine wanda nayi bayani, sakacin talakka kuma shine' har yanzu talakkan Nigeriya mafi yawa, wallahi basu yarda ma da ita wan'nan cutar ba.

'Yan'uwana talakawa! Wallahi wan'nan cutar gaskiya ce! Wallahi kuma tana kisa, wallahi idan baka yi hoɓɓasa na kariyar kaiba zata iya shafarka. Don Allah kayi ƙoƙarin kare kanka da iyalin ka tunda gwamnati ta gaza.

Zanyi magana da Musulmi anan kai tsaye saboda ni shine kuma shi nasani, 'yan'uwa abokan halitta kiristoci suma nasan tunda addinin su saukakke ne daga Allah(T) tayiyu a maganar da zanyi tazama ɗaya.

Amatsayin mu na musulmi zamuga dukkan shawarar likitoci dangane da kariyar wan'nan cuta, duka dai tsafta ce, mu musulmi kuwa agurin mu tsafta cikon imani ce. Yanzu ni musulmi har sai ance inyi tsafta?

Likitocin lafiya sunce kadunga wan'ke hannuwanka da sabulu ko da sinadarin wanke hannu, duk'idan kayi mu'amula da mutane ko kuma bayan wasu mintina, Sama da shekara dubu da ɗari hudu Annabi yana umartan mu da wanke hannuwa idan mun fito daga ban ɗaki, da ƙasa ko da toka, saboda shima akwai sinadari acikin ta, ƙarewa ma duk'musulmi cikakken musulmi yana wanke hannuwansa sau biyar a rana(Sallah).

Likitoci sunce mudaina Atishawa acikin mutane, idan kuma zamuyi mu rufe baki da hanci, Annabi(s.a.w.) sama da shekaru dubu da ɗari huɗu yana umartar mu da mu ƙaurace ma jama'a idan zamuyi Atishawa don gudun kada mucutar dasu, idan kuma munyi muce Alhamdulillah.

LATSA NAN👇
Ranar lafiya ta duniya: Qalubale ga gwamnatin Nijeriya
Happy birthday to the golden son of 21st century Sheik Zakzaky
Imam Mahadi (Ajtfs): Wacce tambaya kake tsoro Imam yayi maka???

Likitoci sunce ka taƙaita zirgazirga domin gudun yaɗuwar cutar, sama da shekara dubu da ɗari huɗu Annabi(s.a.w) yace idan annboba ta sauka gari, kada kashiga garin shikuma wanda ke garin kada yafita.

S.A.W. yakamata ace kai Musulmi kai zakaba likita wan'nan shawara kaida kake da Annabi,(S) kuma shugaban likitocin duniya. Ba likita da ya karanta iliminsa wajen Nasara zai fadimaka haka ba. Ba naraina Ilimin likitocin bane a'a inanufi mu musulmi muke da wan'nan ilimin tun kafin a haifi Uwar CORONAVIRUS.

Don haka Inaga yakama ta mu' musulmi talakawa don Allah mukula kuma mu kare kanmu daga wan'nan Attajirar cuta, idan kuma ka sake ta fara kamaka, kai talaka, to ba sai nace komi ba, nasan talakka baka da kuɗin fita waje neman magani, masu kuɗin ma dai yanzu ya suka cika? Duniyar tazama kamar filin ƙiyama, Nafsi Nafsi!! Kowa takansa yake babu mai taimako.

Kuma kaga dai yanda ƙasar ka take babu, tayi yawa acikin ta ba wuta ba ruwa ba tsaro ba kiwon lafiya babu ingantaccen ilimi, babu kudi.

Kuma Talakka kasanya aranka cewa wallahi babu abinda Gwamnati zata'iya yimaka tanadai faɗi ne kawai dan kaji daɗi.
Yo inba haka ba, naka' ma da kake juyawa ta hana inaga nata? Ka fito nema ankashe ka ba'ayi tunanin cewa yunwa ce ta fiddoka ba, ba'ayi tunanin gidanka da yaran da basu ma san babu ba.

Idan yaro yacemaka yunwa yakeji kace babu abinci sai yace maka abashi babun yaci, amma duk'da haka idan ka fito ka nema sai akashe ka.

Batare da tausayin 'ya'ya ko matan da kabariba.
Don haka talakka kasani cewa baka da gata kayi addu'a kakula da kanka kakoma ma Allah. IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post