Ranar Lafiya Ta Duniya: Qalubale ga Gwamnatin Nijeriya




Ranar 7 ga watan Afirilun kowace shekara, rana ce da aka kebe domin tunawa da kafuwar hukumar lafiya ta duniya wato WHO a shekarar 1948, kimanin shekaru 72 da suka gabata ke nan.

Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Hukumar lafiya ta Duniya wato WHO tana gudanar da aikace-aikacen ta na jin ƙai aduk faɗin duniya, musamman,ma' ga mata da ƙananan yara domin daƙile yaɗuwar cututtukan da ke bazuwa, bama kamar a yankunan Afrika.

Nigeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu tasowa da hukamar ta WHO ta maida hankali a kanta duba da yanayin da ƙasar take ciki, na ƙalu balen BokoHaram da yanayin na rikice rikece bama kamar a Arewacin ƙasar.

Bincike ya tabbatar da cewa duk'ƙasar da ke fama da yawan faɗace faɗacen Addini ko ƙabilanci, ko kuma halin yaƙi tafi fama da matsalar kiwon lafiya, kasantuwar rashin kwanciyar hankali da bazai bada dama afuskanci ɓangaren lafiyar gadan gadan ba.

Nigeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da cututtuka, irinsu'Zazzaɓin cizon sauro(Malaria)Lassa fever, Ciwon hanta(Hepatitis B) Tarin fuka,(T.B) Shan'inna (Polio) Amai da gudawa,(Kwalara) Kyanda(Measle) da sauran su.

Amma zamu'iya cewa cikin ikon Allah da taimakon hukumar WHO da sauran ƙungiyoyin lafiya, na gida da na waje, haɗin guiwa da Gwamnatin ƙasa, kusan anci ƙarfin waɗan'nan cututtuka kashi saba'in ko tamanin cikin ɗari.

LATSA NAN👇
Sister a Social Media Fita Na Ɗaya (1)
Hikima kayan mumini Part (4)
Dokoki 17 da ke kan mace saliha Fita Na (16)
Nazari akan Rayuwar Aure Fita Na Biyu (2)

Sai dai, ba a nan gizo ke saƙa ba. Shin waɗan'nan cututtuka da suka addabi ƙasar mu Nigeriya sun tafi kenan? Allah yasa haka. Idan suntafi, shin mun riga mun tsira daga ire-iren waɗan'nan annoba? Nasan mai karatu zai bani amsa da, a'a.

To idan a'a minene mafita a ƙasa irin Nigeriya adai dai lokacin da hukumomin lafiya na duniya Irin su WHO,Unicef, da makamantan su, suke ta kwashe yanasu yanasu, suna barin Nigeriya da wasu ƙasashen Afirka, kasantuwar taɓarɓarewar tattalin arziƙin da duniya ke fuskanta?

INA MAFITA? a irin wan'nan yanayi da, Duniya ke fuskantar wani, babban bala'in annoba ta CORONAVIRUS da tazama Musibar da ta gagari masana, masu binciken cututtuka da magun guna na duniya.

CORONAVIRUS-Ba baƙuwar cuta bace, saboda masana masu ilimin fulosafa na duniya sunyi bayanin ta dakuma shekarar da zata ɓulla, wanda har yasanya wasu daga cikin al'ummar duniya suke ganin, anƙirƙireta ne, an ɓoyeta har zuwa wan'nan lokacin.

Ta janibin mu musulmi kuma (wasu) muna kallon ta a matsayin Ibtila'i ne ko Annoba, ce Allah ya sauko, a matsayin horo ga mutanen duniya, sakamakon zubda jinin Al'uma da wasu Gwamnatocin duniya keyi babu gaira babu dalili.

To koma minene dai yanzu ga CORONAVIRUS ga Nigeriya, kasar da tun tuni tana cikin tsananin Ciwon cin hanci da rashawa da ya mamaye duka ma'aikatun ƙasar.

NIGERIA-Tana cikin tsananin ciwon annobar Azzaluman Shuwaganni da basu da imani ko mizƙali zarrati, basa ƙaunar ƙasar basa kishin talakkan ƙasar, bakuma su iya yima ƙasa da talakkan ƙasa abinda zai masu addu'a saidai suyi mashi abinda zaice Allah wadarai.

NIGERIA-Ƙasar da keda shuwagabannin da sunfi ƙaunar karen da kemasu gadin kofa bisaga talakkan ƙasar, akan karensu suna iya kashe tallakn ƙasar su.

NIGERIA- Ƙasar da mukafi kowace ƙasa a Afrika arziƙi, kuma mukafi kowa talauci, inda talakkan ƙasar ke kashe kansa saboda yunwa, ƙasar da talakka ke cin abinci sau ɗaya a rana, ƙasar da mafiya yawan talakawan ta sunada ciwon Ulcer saboda ba'aci aƙoshi.

NIGERIA- Ƙasar da Shuwagabannin ta kowa ɓarawo, sai nadiran, ƙasar da shiwagabannin ta suke gogoriyon shiga asibitocin ƙasashen waje saboda ciwon ƙunne, ayayin da ake binne talakka a ƙabari idan yayi doguwar suma, saboda rashin kayan awon gano ya mutu ne, ko yana raye?

NIGERIA- Ƙasar da jami'an tsaro ke kashe 'yan ƙasa babu gaira babu dalili badon komi ba sai saboda sun samu goyon bayan gwamnati, ko akama talakka a garƙame a gidan kaso har amanta dashi, koda kotunan ƙasa sunce asakeshi.

Kada in kauce daga asalin maganata, ina magana ne akan Ranar lafiya ta duniya, ranar da Gwamnatocin duniya suke duba 'yan ƙasar su marasa lafiya da yimasu gata, da damuwa da matsalolin da ke damun su, domin magance masu.

Ni dai ƙasata' narasa wan'nan gatan dani da matata, yau shekara huɗu da watanni inafama da matsanancin ciwo ajikina, wanda Gwamnatin ƙasata tayi sandiyyar sa, amma duk da haka takamani ta ɗaure, narasa 'yanci na, alokacin da duniya tayi tsit bisa zalunci da akaimani.

NIGERIA-Da talakkawa raunana suma sunyi tsit, wasu ma sunacewa Allah ya ƙara saboda rashin sanin ciwon kai, da rashin sanin cewa, Azzalumar Gwamnati tana yaƙi ne da dukkan ɗan ƙasarta wanda bai yarda da zalunci ba, ba Ni El'zakzaky ba.

Idan kanaso ka san haka ƙai tsaye, to kayi bara'a wa zalunci, kagoyi bayan Adalci, kaga idan zaka tsira.

Yauwa! Ya ishemu musali, a garin kaduna inda aka ƙaƙabama talakka dokar ta ɓaci kada yafito ko ƙofar gida, bama maganar ibada ko kasuwanci ba, talakawa sukaga alamar yunwa zata cimmasu, suka fito domin su samu ɗan abin da zasu sama cikinsu, anan take Azzaluman jami'an tsaron Najeriya suka kashe sama da mutum biyar.

Ba tare da tunanin cewa waɗanda aka kashe ɗin nan fa musifar yunwa ce ta fiddo su, domin su, samu' su ci da iyalai da 'ya'yan su, taɗauro ma sunada yara ƙanana waɗanda basu san babu ba.

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNA!
Lallai akwai fushin Allah aƙasar nan kuma wallahi bazaidaina bibiyar muba sai mun tuba, mun nemi gafarar waɗanda muke zalunta da harshe, ko da idanu, ko da hannu, ko da ƙarfin mulki.

Akarshe ina fata wan'nan rubutu nawa yazama nuni ko dawowa haiyacin talakka ayayin da yake karantawa.

Tunda yaune ranar lafiya ta duniya ina kyakykyawar fata da addu'a, ga duka Al'umar duniya masu lalura ko wace irice aduniya musulmi da kirista dama duk mai son zama lafiya da adalci Allah ta'ala ya yaye masa.

TUNATAR WA

A rinƙa amfani da Face Mask tare da Hand Sanatizer (Man wanke hannu) ana wanke hannuwa, bayan anyi ma'amala da Mutane, a guji taɓa fuska da hanci a kaurace ma shiga cunkosan Mutane idan kaji alamu mai kama da mura, musamman idan kayi tafiya zuwa ƙasar waje ka dawo, ka keɓe kanka tsawon sati biyu. Daga karshe a hada da Addu'a.

Allah ya tsare mu daga Cutar nan ta CORONAVIRUS.

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Zaharaddeen Mziag
07/04/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post