An kashe masu yi wa 'yan bindiga leken asiri biyu a Katsina



An kashe wasu mutane biyu Ibrahim Maye da Bishir Mai Laya da ake zargin suna daga cikin manyan masu yi wa 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane leken asiri a Katsina. An kashe mutane biyu ne a karshen makon da ya gabata a yayin da suke kokarin isar wa masu garkuwa da mutane sako a kusa da dajin Kasuwar Gora a karamar hukumar Safana.

Dukkansu biyun sun fito ne daga kauyen Hayin Gada a karamar hukumar Dutsinma na jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Rahoto daga majiya ta ce da isar su dajin, sun hadu da wani tsohon dan leken asiri mai suna Amale amma ba su san cewa ya tuba ya rungumi shirin yin afuwa ga gwamnatin jihar ba.

Duba da cewa ba su san ya dena sanaar ba, ya mika musu sunaye da hotunan mutane uku da za a yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa. Sunayen da aka bayar na yan kasuwa, Abu Farar Waina da wasu mata biyu an kirkire su ne kawai saboda a kama 'yan leken asirin amma babu mutane masu wannan sunan. Daga baya an gano cewa wannan tarkon da aka kafa ya yi sanadin kama wasu manyan yan leken asiri da suka amsa cewa suna da hannu wurin sace jami'in kwastam, Nasiru da wasu 'yan biyu maza a kauyen Gizagawa.

Bayan sun tona asirin sauran 'yan leken asirin, an kashe mutanen biyu sannan aka aike da gawar su zuwa wani tubabben dan bindiga, Kachalla, wanda ya mika gawar ga jamian tsaro. Majiya daga yan sanda ta ce tuni an fara farautar sauran 'yan leken asirin bakwai da aka ce suna aiki a kauyukan Dutsinma da Kagara. Da aka tuntube shi, Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya yi alkawarin zai yi bincike a kan lamarin.KARANTA MUHIMMAN LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/

IDAN KUNADA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KUTURO MANA ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post