Qissar Kofaton Jakin Annabin Isah (As)


Ma'asumah Nigerian News Update

Daga: Bin Haroun Sigau

-An ruwaito daga Imam Ali Ibn Hussain Zaynul Abideen (As) yace,

-Lokacin da aka kawo kan Imam Hussain ga Yazidu, yayi zaman shan giya, ya kawo kayin Hussaini (As) kusa dashi kuma zaisha giya a gabansa. Wata rana, ɗan aike na Sarkin Rome yana wajen a wani zaman Yazidu, kuma yana cikin manyan masu daraja a ƙasar Rome.

-Yace, yakai sarkin Larabawa! Wannan kan wanenen? Yazidu yace masa: Menene damuwarka da wannan kan? Sai yace, Inna koma Sarki zai tambaye ni game da duk abinda na gani. Don haka zanso in bashi labarin wannan kayin, da mai shi don sarkinmu yayi tarayya dakai cikin jin daɗi da farin ciki.

-Yazidu yace, wannan kayin Hussaini ne ɗan Aliyu Ibn Abu Talib. Mutumin Rome yace, wacece mahaifiyarsa? Sao Yazid (L.a) yace Fatima ƴar Ma'aikin Allah. Kristan yace, Tir dakai da addininka! Inna da addini fiye da naka, haƙiƙa, mahaifi na yana daga zuri'ar Dawud (As), kuma akwai ƙarnoni tsakanin Dawud (As) da Babana.

-Amma Kristoci suna girmama ni, sukan ɗebi kasa daga wajen dana taka domin neman albarka sabida Babana, a matsayin zuri'ar Dawud (As). Amma kai ka kashe ɗan ƴar Ma'aikin Allah, baya ga tsakaninsa Mahaifiyarsa ce kaɗai! Wannan wanne irin addini ne kake dashi?.

-Daga nan sai yace da Yazidu (L.a) kaji labarin cocin kofato? Sai yace gayamin don in sani, Yace, akwai kogi tsakanin Oman da China da yakan dauki mutum shekara kafin ya tsallaka. Babu mazauni sai wani gari a tsakiyar Ruwa. Wajen yana da tsawo da faɗi tamanin-tamanin ta ko wanni sashi, babu wani birni a duniya daya kaishi girma, kuma Kafur da jan karfe akan zo dashi daga cen ne.

-Bishiyoyin wajen 'Aloe' ne da 'Embergris' yana hannun Kristoci ne. Babu wani sarki ko sarauniya dake da iko dashi sai su, akwai Coci na da yawa a cikin garin, mafi girma shine; Cocin Kofato. Akwai wani ƙaramin akwati a maƙale da Ƙofato, suna tunanin Kofaton Jakin da Isah ɗan Maryam (As) yake hawa ne. Sun ƙawata muhallin akwatin da gwal da Silki mai kauri a waje tsarkakakke.

-Duk shekara Kristoci sukan yi aikin Hajji gareshi, suna zagayeshi, sumbatarshi da miƙa addu'o'insu ga Allah, Maɗaukakin Sarki. Wannan shine hanyarsu da al'ada ga Kofaton Jakin da suke tunanin Isah Ɗan Maryam (As) Annabinsu, yake hawa. Amma ku kun kashe Ɗan ƴar Annabinku? Allah bazai albarka ce ku ba da addininku. Yazidu (L.a) yace, Ku kashe wannan Kristan kada yasa a bijire min a wannan birnin, da Kristan ya fahimci haka yace ga Yazidu, kana son kasheni ne? Yazidu yace, Eh.

-Yace, yanzu nasan dalilin ganin Manzon ku a mafarkina danai daren daya gabata. Yace min; Ya kai Krista! Kana daga cikin mutanen Aljanna! Nayi mamakin abinda ya faɗa gare ni, yanzun na shaida "Babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma Muhammad Manzon Allah ne (S). Sai yai tsalle zuwa ga kan Imam Hussain (As) yana mai rungumarsa yana sumbatarsa yaɓa kuka har aka kashe shi.

Duba Biharul Anwar, Mj 45, Shafi na 144.
-Allah ka ƙara ninninka la'anta ga makasan Imam Hussain (As) da dukkan Musulman duniya baki ɗaya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post