Siffofin Yan Shi'a


Ma'asumah Nigerian News Update

Tare da ┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

-Ali Ibn Husain Al-Sa'dabadi ya ruwaito daga Jabir Ju'ufi cewa Abu Jafar (As) yace,

-Yakai Jabir, Kana tunanin ya isa ga waɗanda ke da'awar su Ƴan Shi'a ne suna ƙaunarmu, mu iyalan gidan Manzon Allah (S)?

-Na rantse da Allah, ƴan Shi'armu su kaɗai ne suke tsoro da biyayya ga Allah, Alaminsu sune tufafi, biyayya, cikakkiyar yardar da umurnin Alllah, azumi, sallah, biyayya ga iyaye, taimakon marayu, taimakon makusanta musamman talakawa, gaskiya, karatun Qur'an, da kiyayen ambaton mutane saidai game da alkairinsu, bugu da ƙari sune mafi aminci a cikin yarukansu.

-Jabir yace, yakai Dan Manzon Allah (S), bamu san wani wanda ke da waɗannan halaye ba.

-Imam (As) yace, A'ah ya Jabir, baka fahimci al'amaran ba, ya isa ga mutum yai da'awar yana so kuma yana bin Ali (As), A lamarin gaskiya, idan yai da'awar yana son Manzon Allah wanda yake mafi soyuwa ga Imam Ali (As).

-Amma baya bin sunnar Manzon Allah kuma baya bin umurninsa, wanna da'awar soyayyar tasa ta zama aikin banza. Saboda haka yakamata kaji tsoron Allah kayi aiki don samun abinda kake nema.

-Babu wata dangantaka tsakanin Alllah da kowa. babu wanda yafi wani a wajen Allah sai mai tsoronsansa da taƙawa.

-Yakai Jabir, babban abinda bawa zaiyi domin Allah ya so shi, shine yi Masa biyayya damu iyalan gidan Manzon Allah (S). Kada ka ɗauki hanyar kira zuwa ga rashin samun ceto daga shiga gidan wuta.

-Kamar yadda, babu wani a cikinku dake da kokonto gameda da rahmar Alllah (T). Duk wanda yayi wa Allah biyayya shine Almajirinmu, duk wanda kuma yaƙi biyayya ga Allah, to, Maƙiyinmu ne. Biyayya garemu baya samuwa sai da aikin haƙuri da taƙawa.

-Allama Majlisi yayi sharhi: Wannan yana nufin babu wata abota tsakanin Allah da Ƴan Shi'a saboda bazai yafe musu zunubi ba kamar yadda bazai yafewa sauran al'umma ba.

-Hakan ma yana nufin babu wata abota tsakanin Allah da Imam Ali, sabida bazai yafewa mabiya Ali ba tare da ya yafewa mabiya Manzon Allah (S) ba.

Misali
..........

-Waɗanda suka aikata saɓo iri ɗaya, dabida haka, dangantakar Allah da bawansa kawai, shine yima Allah (T) biyayya da tsoro uƙubarsa. A wannan hanyar, Imamai Allah ya ƙara musu yarda sune mafi soyuwar mutane a wajen Allah (T).

ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALI MUHAMMAD............

-Don ƙarin bayani a duba

Amali na Sheik Saduq, Shafi 499 da Amali Na Sheikh Tusi, Shafi 735/1535. Sai kuma Mishkatul Anwar, Shafi 58, da Biharul Anwar, 70:79 Hadisi na 4.




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post