Tarayya da mutane ma'abota addini



Ma'asumah Nigerian News Update

Daga: Bin Haroun Sigau

ibn Ibrahim ya ruwaito daga Muhammad bin Isa daga Yunus daga Lukman wayayye wanda ya fadi wadannan kalmomin ga yaronsa:

“Ya Dana! Ka zabi wajen zamanka, idan ka sami mutane masu magana don Allah, mai girma da daukaka, ka zauna dasu. Idan dama kai masani ne zaka karu daga iliminka kuma in kai mara ilimi ne zasu karantar dakai.

Ko ba komi, Allah mai girma da daukaka zai rufe su da rahmarsa kaima zaka kasance cikin rahma tare dasu. Idan kuma kaga mutane wadanda basu Magana dangane da Allah, kada ka zauna tare dasu sabila da koda kaso kasan wani abu daga garesu bazai amfanar dakai ba, idan kuma kai mara ilimi ne zasu kara dilmiyar dakai.

Ko ba komi, Allah zai lullubesu da azabarsa kuma zaka kasance tare dasu a cikin wannan azaba din. Al-kafi, babi na 8, Hadisi mai lamba na 1.

-Yazo a wata ruwayar kuma Muhammad ibn Isma’il ya ruwaito daga Al-Fadal ibn Shadah daga Ibn Abu Umair daga Mansur ibn Hazim daga Abu Abdallah(as) yace;”Manzon Allah tsira da amanici su kara tabbata gareshi’ yace; “Tarayya da mutane ma’abota addini daraja ne a wannan duniyar da kuma rayuwa ta gaba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post