Gare mu matasan harka


MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Abbagano ✍️

Da farko zanyi Kirane zuwa ga matasan mu, na harka islamiya karkashin jagoran cin uban ahamad sayyid Ibrahim zakzaky.

Yana da kyau hankalin mu yadawo jikin mu domin mutsaya muyi abinda yadace muyi, shin menene zamu iya? Kuma shin mene muke yi?? Kuma mene ne muka gazayi??

Ta fuskacin ilimi shin wanne hali muke ciki Yan uwana matasa?? Idan karatun boko kake shin wanne mataki kake Kai?? Ko kakai matakin dazaka iya Samar da abinda Babu shi?? Idan karatun addini kake shin kagama Zama ashmal ne??

Sau dayawa halin da mu matasa mu ke ciki, akwai abin takaici sosai, zakaga dalibi Dan harka islamiya mabiyin imam Ali Amman bai maida Kai akan karatun dayake' ko mun manta wa muke bine?? Mun manta wanene imam Ali (as) ne?? Babu yadda za'ai ace mabiyin imam Ali na hakika yazauna bai tinanin abinda ya dace,

A dukkan wani bangare dakake na karatu Yana dakyau ka maida Kai kayi don kataimakawa harka islamiya dashi'  domin ita harka Tana bukatar komi.

GARE KU YAN HARKAR DA BAKWA NEMAN ILIMI.

lalle akwai abin kunya da takaici, ace ansamu wani daga cikin matasan harka baya neman ilimi,na boko Kona addini, ko mun manta da maganar Allah ne dayace :-

قُلْ هَلْ يَسْتَوِي الَّذِينَ يَعْلَمُونَ وَالَّذِينَ لَا يَعْلَمُونَ ۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُولُو الْأَلْبَابِ

Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.

قال عليه السلام :( لو أتيت بشاب من شباب الشيعة لا يتفقه لأدبته)

Imam bakir (as) yake cewa: da za'azo masa da matashi daya daga cikin matasan Shi'a baya neman limi  da sainai masa ukuba.

To Kai Dan uwana matashi kaji abinda Allah da imaman mu suke fada dangane da rashin neman ilimi, to shin yakamata muzauna haka??

Yana dakyau muyi tunani mu Tsaya muyi abinda za mu iyayi, kafin Lokacin mu yakare,  don shi lokaci baya jira.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post