Kwalliya: Yadda zaki magance matsalar bushewar fata



Ma'asumah Nigeria news update

M.N.U 030

Sakina Ahmad & fertemerh shaheder


A darasinmu na yau za mu yi duba ne akan yadda za ki magance matasalar bushewar fata domin ita ma busasshiyar fata tana bada matsala ga nagartacciyar kwalliya.

BUSASSHIYAR FATA: Za ki iya gane busasshiyar fata ce da ke da wadannan alamun: Saurin bushewar fata a lokacin iska ko dari, yawan yin saba, kyasfi, fashewan lebe a lokacin iska ko dari, yawan jin kaikayi da kasancewar fata ta yi fururu kamar an bada miki garin fulawa, yamutsewar fata da sauransu. Ko shakka babu irin wannan fatar ta fi kowace iriyar fata bukatar gyara, kuma wannan darasi ya zo mi ki da hanyoyin magance matsalar bushewar fata.


Hanyoyin Magance Matsalar Bushewar Fata.


ki daina wanka da ruwa mai zafi domin yana taimaka wa wajen tatse maikon da ya saura gareki ki daina zama a cikin rana mai zafi, kayan sawarki ya kasance mai laushi ba mai gautsiba ki daina yawan barin jikinki ko wani bangare na jikinki a bayyane musammam a lokacin iska Leben ki ya kasance a koda yaushe ya kasance cikin mai ko basilin ko lip gloss mara kala. Ki kiyayi jambaki na wani dan lokaci ko kuma daga kin gama abun da za ki yi da Jambakin ki goge ki sa lip gloss din ki, idan za ki yi burushi da safe ki wanke har da labbanki domin za su yi laushi kuma mataccen fatar leben zai fita. Sai dai ba a goga burushin da karfin tsiya. ki dinga yawan shafa madarar yoghurt a fuskar ki ko madara idan ta bushe, sai ki dauraye da ruwan sanyi sosai kada ki rika yawan durje fuskarki kuma kada ki yawaita amfani da Sabulu da yawaki rika yawan amfani da mayuka da aka yi su da dan itaciyyar APRICOT  ko kuma ya kasance da akwai shi a ciki musamman ma ga kanki, ki sayi OATS ki nika shi ya yi laushi sosai idan za ki yi wanka sai ki dibi chokali daya ki zuba a kofi daya na ruwan zafi ki juya idan ya narke sosai sai ki zuba a ruwan wankanki juya da kyau (ruwan wankanki ya zama shi ba mai sanyi ba kuma ba mai dumi ba.Idan kin gama kada ki goge jikinki ki bari fatarki ta shanye ruwan jikin naki.Avocado (piya) ki cire bawon ki yar sai ki dama ta yi laushi ki shafeta a fuskar (kina lailaya fuskarki a hankali) idan ya bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi sosai ki raba ruwan wankan ki biyu, idan kin gama wanka da daya sai ki shafa basilin (vaseline) ko man kade sannan ki watsa sauran ruwan a jikinki. Za ki sake shafa mai in kin fito ki yawaita shafa wa fuskar ki da hannu da kafarki mai duk bayan kowace sallah domin sun fi komai bushewa a jikin ki idan za ki shafa mai a fuskarki, bayan kin lakato man a hannunki kin mutsuttsika sai ki fara tafa hannunki duk biyun akan fuskar ki a hankali ko ta ina har sai man ya shafu a haka.

Kwalliya A Lokacin Zafi

Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da blackheads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa.

Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi:

•Hoda; Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.

•Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.

•Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.( bakaken kaya irin na kwalliyar gida, ba hijabi. Kar ki manta muna darasin kwalliya ne, ita kuma kwalliyar nan a gida ake yinta don farin cikin mai gida, ba wai kiyi Kwalliya ki fita ba.)

•A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.

•Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.

Yadda Ake Kwalliyar Fuska

Mata da dama  musamman ma wadanda za su yi aure sukan biya kudi mai yawa domin a yi musu kwalliyar fuska. Ba shakka daga an ga wanda aka yi wa wannan kwalliya lallai za a ce kwalliya ta biya kudin sabulu. Ina so in sanar da ku cewa wannan kwalliyar za a iya yin ta a gida idan akwai kayan aiki.

Da farko dai ana so a wanke fuskar da sabulu sannan a jira ta bushe kafin a shafa mata komai.

Ana so a samu ruwan goge fuska (cleanser) a goge fuskar da shi da auduga.

Bayan an yi hakan, sai a shafa man SPF (sun protection fuemula).

A samu hodar foundation  dai-dai kalar fatar mutum sannan a shafa.

A samu powder a sake shafawa.

Sannan sai a samu reza ga wanda ke da cikan gira sai a aske shi kadan.

A samu gazal din mac guda biyu; daya baki daya kuma ba baki sosai ba sannan a zana girar da shi.

Bayan haka sai a samu ‘concealer’ da na ‘eye shadow’ da burushin ‘eco tools’ da burushin ‘eyeliner’.

Sai a fara taje giran da burushin ‘eyeliner’

Sannan sai a zana girar da gazal din mac da dayan mara baki sosai a hada su.

Bayan an shafa sai a sake taje su da ‘eyeliner brush’ din.

Sai a dauko ‘brush sigma E65’ a debi eye shadow mai duhu a sake shafawa a girar.

A sake dauko gazal din a sake zana giran sama da kasa.

A shafa ‘concealer’ din da ‘brush E65’ din dai-dai kalar fatar mutum.

Sannan sai a shafa ‘eye shadow’ kalar kayan da za a saka.

Sai a shafa jan baki.

Hanyoyin Kulawa Da Fuskarki

Wanke fuska kafin ki kwanta bacci a kowane dare:



Me ya sa ya kamata a rika wanke fuska kafin a kwanta barci?



Na san kowa zai so ya ji amsar wannan tambaya. Wanke fuska na da matukar muhimmanci ga mace da namiji. Mata da dama ba su damu da yin wanka da daddare kafin su kwanta barci ba. Wata ma tun kwalliyar da ta yi da daddare ta fita hira wajen saurayinta haka za ta shigo gida ta kwanta barci ba tare da ta wanke fuskarta ko kuma ta yi wanka ba. Don haka ya kamata ki canza, ki rika wanke fuskarki kafin ki kwanta barci saboda:

Wanke fuska ko wanka kafin a kwanta na sanya kwanciyar hankali da samun barci mai dadi.Idan mutum ya kwanta ba tare da wanke fuska ba, mayukan da ya shafa a fuskarsa na taruwa su fitar da manyan kuraje, inda sai an yi da gaske kafin a rabu da su.Yana da kyau a wanke fuska da sabulun wanke fuska, domin fuska ba ta cika kwari ba kamar sauran fatar jiki.Kada a manta a rika goge fuska da sinadarin ‘cleanser’ kafin a kwanta barci.Ki yi amfani da ‘cleanser’ da ta dace da fatarki kafin a fara amfani da ita wajen wanke fuska.Rashin wanke fuska kafin a kwanta na rage wa mace kyau, domin idan kurajen suka feso a fuska kan samu matsala ko ta canza.Rashin yawan wanke fuska na janyo maruru a fuska.Rashin wanke fuska ko wanka na janyo fitowar kyasbi a fuska, don haka sai a kiyaye.

Ma'asumah Nigeria News Update

Tare da Wakilanmu na kano shaheder fertemerh & Sakina Ahmad

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post