Karen Armstrong: Duniya ta tsani Musulunci ne saboda sun ga shine addini mafi rinjaye a doron kasa


MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Daga: Bin Haroun Sigau

Musulunci addini ne mai cike da dabaru. Mutane masu fahimta ne kadai suka fahimci addinin da kyau. A wata tattaunawa da aka yi da wata marubuciya mace wacce ta karba lambobin yabo, ta bayyana cewa addinin ne mai matukar rinjaye.


Matar wacce marubuciya ce ta kare Musulmai da Qur’an. Ta ce mutane sun tsani addinin ne saboda suna tunanin yana da rinjaye. Babbar marubuciyar mai suna Karen Armstrong ta sanar da hakan ne yayin da aka tattauna da ita a kan Musulunci.

A lokacin da aka tambayeta a kan ta’addanci a Musulunci, marubuciyar ta ce Qur’ani ba magana kadai yai a kan jihadi ba.

Tattauanwar ta bayyana ne a El Mundo a kan yadda marubuciyar ta Musulunci ke fuskantar kalubale mai tarin yawa saboda karfin rinjayen shi a duniya.

Kamar yadda Armstrong ta bayyana, Qur’ani ya kunshi gina jama’a ne masu madaidaiciyar dama amma sai ake amfani da shi wajen kare ta’addanci.

Ta ce ayoyin jihadi duk ba a fara amfani da su ba sai bayan shekaru 400 bayan da wayewar addinin Musuluncin.

‘Bayan shekaru 400 da mutuwar Annabi Muhammad, lokacin da gabas da yamma suka hare su, shugabannin sai suka ba wa jama’a karfin guwair ramawa.” Marubuciyar ta ce.

“A yau mutane sun tsani Amurka ne saboda ta fi kowacce kasa karfin rinjaye a duniya. Muna tsanar wasu abubuwa da muka gani a rayuwarmu,” marubuciyar ta ce.

Tsohuwar ma’abociya akidar katolika ta addinin Kiristar ta sadaukar da rubuce-rubucenta ne a kan binciken da kamanceceniyar addini.

Tsohuwar jigo a addinin Kiristar mai shekaru 75 ta fara ne da wallafa tarihin annabi Muhammad a 1991, kamar yadda jaridar the Guardian ta wallafa.

Marubuciyar ta yabawa yadda musulmai da ke Amurka suka dau rubutunta da matukar amfani a matsayinta na babbar marubuciya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post