Ziyarar Sheikh Ya'aqub Yahaya Katsina Ga Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @

A yau ne lahadi 2-2-2020 aka kammala Mu'utamar na dandalin matasa karo na 27 a babar Markaz dake garin garin Bauchi.

Wannan  Mu'utamar an shige shi daga ranar juma'a 31th January aka qare shi yau lahadi 2-2-2020.

Sheikh  Ya'aqub Yahaya Katsina ne ya kasance babban baqo mai jawabin rufe.

Bayan tashi daga taro ne shehin malamin ya ziyarci baban shehin malamin dariqar Tijjaniyyah As-Sheikh  'Dahiri Usman Bauchi,da,ke zaune a garin Bauchi.

Wannan ziyara ta girmamawa,ne irin wacce Sayyid Ibrahim  Ya'aqub  El-Zakzaky  (H ) ya koyar da su.

Haqiqa malamin ya nuna cewa shi haqiqanin mabiyin Sayyid  Zakzaky (H )ta hanyar ayyukansa da kuma zantukansa, domin kuma yana aikata tarbiyyar da jagora ya dora su a kanta.



Shi kuma Shehin malamin ya nuna matuqar jin dadinsa na ganin wannan ziyara ta girmamawa, kuma yayi addu'ar Allah (T )ya qarawa jagoranmu lafiya da kuma kwato mana shi daga hannun wadannan azzalumai .

Daga wakilan mu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

    08126385470

~2nd February , 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post