HADISAI GUDA 40 NA IMAM ALI (AS)!!!!

WASU FITATTUN HADISAI NA IMAM ALI (AS) HAR GUDA 40.....
1-Imam Ali[AS] ya ce, “ Duk wanda ya gyara tsakaninsa da Allah to Allah zai gyara tsakaninsa da mutane,duk wanda ya gyara al’amarin lahirarsa to Allah zai gyara al’amarin duniyarsa.”


2- Imam Ali[AS] ya ce, “ Ya kai ]an Adam idan ka ga Allah Ta’ala yana yi maka ni’imomi alhali kana sa~a masa to ka yi hankali.” Wato zai kasance kenan istidraji ga mutum.


3- Imam Ali[AS] ya ce, “ Idan ka samu iko kan ma}iyinka ka yi afuwa gareshi a matsayin godiya ga Allah kan wannan iko da ka samu akansa.


4-Imam Ali[AS] ya ce, “Mutane basu bar wani abu ba na al’amarin Addininsu saboda mas’lahar duniyarsu face Allah Ta’ala ya bu]e masu abunda ya fi haka tsanani.”


5- Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda yasa kansa a in da za a iya tuhumarsa,to ka da ya zargi duk wanda ya munana masa zato.”misali mutum yaje in da ba a tsamanin samun ma’abucin addini ko mutumin kirki a wajen.


6-Imam Ali[AS] ya ce, “Mafificin ayyuka sune wa]anda ka tilasta kanka wajen aikatasu.” Wato ayyukan da mutum yayi mujahada wajen aikatasu,ayyukan na ibada ne ko umarni ko hani.


7-Imam Ali[AS] ya ce, “Ina mamakin wanda yake cire tsamanni daga rahamar Allah Ta’ala alhali ga istigfari.”


8-Imam Ai[AS] ya ce, “Allah Ta’ala yana da ha}}i ga kowace ni’ima da yayi ma mutum,wanda ya bada ha}}in sai Allah ya }ara masa,wanda kuma bai bayar ba to akwai yiyuwar ni’imar ta gushe.”Ha}}in ko wace ni’ima da Allah yayi ma mutum shine godiya ga Allah kanta,ya kuma kasance ka da mutum yayi amfani da ni’imar da Allah yayi masa wajen sa~a masa.


9-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda aikinsa ya maida shi baya to nasabarsa ba zata kaishi gaba ba.”Wato idan mutum bai yi kyakkyawan aiki ba a wannan gida na duniya to ranar lahira nasabarsa ba zata amfane shi ba.”


10-Imam Ali[AS] ya ce, “Kuji tsoron sa~a ma Allah a ~oye domin mai ganin ~oyen shine zai yi hukunci ranar }iyama

.”
11-Imam Ali[AS] ya ce, “Zunuban da suka fi muni sune wa]anda wanda ya aikata su bai ganin girmansu.”


12-Imam Ali[AS] ya ce, “ Mai sauraren giba kamar mai gibar ne.” wato a wajen zunubi.


13-Imam Ali[AS] ya ce, “Ku sani duk wanda ya ji tsoron Allah to zai sanya masa mafita daga kowace fitina.”


14-Imam Ali[AS] ya ce, “Fursa tana wucewa kamar wucewar girgije saboda haka ku yi amfani da fursa ta alhairi.”


15-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya yawaita tunanin lahira to sa~on sa  ga Allah zai }aranta.”


16-Imam Ali[AS] ya ce, “Kaso ‘yan uwa akan asasin gwagwadon ta}awarsu.”


17-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya yi ‘yan uwantaka saboda Allah to zai samu ribarta,wanda kuma ya yi saboda duniya to ba zai samu ribarta ba.”


18-Imam Ali ya ce, “Duk wanda ya soka saboda wani abu to idan abun ya gushe zai baka baya.


19-Imam Ali[AS] ya ce, “Mafi alhairin abinda iyaye zasu gadar ma ‘ya’yansu shine Tarbiyya mai kyau.”


20-Imam Ali[AS] ya ce, “Ka zauna da Malamai iliminka zai }aru,tarbiyyarka zata kyautata,nafs ]inka zata tsarkaka.” Nan ana nufin Malamai masu tsoron Allah da kuma aiki da iliminsu. Imam Ali[AS] ya ce, “Komi yana da nashi aibin,aibin ilimi shine manta shi da kuma rashin aiki dashi,aibin ibada shine riya a cikinta,aibin aiki mai kyau shine rashin ikilasi a ciki,aibin Malamai shine son shugabanci.”


21-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya yawaita cin abinci to lafiyarsa zata }aranta,kuma ]awainiyarsa zata yawaita.”


22-Imam Ali[AS] ya ce, “Nine farkon wanda ya amshi sa}on da Manzon Allah ya zo dashi,nine farkon wanda yayi sallah tare da Manzon Allah.”


23-Imam Ali[AS] ya ce, “Wanda ya fiku kamalar imani shine wanda ya fiku kyawawan ]abi’u.”


24-Imam Ali[AS] ya ce, “Imanin bawa ba zai cika ba har sai yaso wanda Allah yake so,ya kuma }i wanda Allah yake }i.”


25-Imam Ali[AS] ya ce, “Imani yana da rukunai guda 4 sune:Dogara ga Allah,fawwala al’amari ga Allah,sallamawa ga al’amarin Allah,yadda da hukuncin Allah.”


26-Imam Ali[AS] ya ce, “Kuka saboda tsoron Allah yana haskaka zuciya yana kuma bu]e rahamar Allah.”


27-Imam Ali[AS] ya ce, “Idanuwa basu bushe ba na rashin yin kuka sai saboda bushewar zuciya,bushewar zuciya kuma abinda yake haifar dashi shine yawan zunubi.”


28-Imam Ali[AS] ya ce, “Tuba na wanke zunubai kuma tana tsarkake zuciya.”


29-Imam Ali[AS] ya ce, “Gogayya ilimi ne mai amfani.”

30-Imam Ali[AS] ya ce, “Ku kawo ma iyalinku wani abu na‘ya’yan itace kowace ranar Jumma’a,saboda su yi farin ciki da ranar Jumma’a.”

31-Imam Ali[AS] ya ce, “Manzon Allah[S] ya aika maya}a to lokacin da suka dawo sai ya ce masu,maraba da mutanen da suka dawo daga }aramin jihadi sauransu babban jihadi,sai sahabbai suka tambaya ya Manzon Allah wannene babban jihadi? Sai ya ce masu shine jihadun Nafs.”

32-Imam Ali[AS] ya ce, “{arya tana kai mutum zuwa ga munafunci,kuma tana gadar da talauci.”

33-Imam Ali[AS] ya ce, “Kashedinka da yawaita Magana domin yana haifar ma mutum yawan zunubi.”misali giba,}arya,annamimanci da sauransu.

34-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya tsare harshensa to Allah zai rufa masa asiri.”

35-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda yake so ya sadu da Allah Ta’ala to ya saki duniya.”wato ya fitar da son duniya a cikin zuciyarsa son da zai shagaltar dashi daga tunanin Allah.

36-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya yabeka da abunda baka dashi to suka ne gareka idan kana da hankali.

37-Imam Ali[AS] ya ce, “Ka 
yawaita tunanin mutuwa da abinda ke bayan mutuwa domin mutuwa }ofar lahira ce.”

38-Imam Ali[AS] ya ce, “Ina mamaki wanda kowace rana rayuwarsa na }arewa amma kuma baya tattalin mutuwa,saboda duk abunda baka san lokacin da zai afko maka ba to ya kamata ka shirya masa kafin yazo.”

39-Imam Ali[AS] ya ce, “Wanda yafi tsananin munafunci a cikin mutane shine wanda ya yi umarni da aiki mai kyau amma kuma shi bai aikatawa,yana kuma hani ga sa~o amma kuma shi bai hanu ba.”

40-Za a kammala wa]annan Hadisai arba’in da aka ruwaito daga Imam Ali
[AS] da wasiyyar da yayi ma ‘ya’yansa bayan da ibn Muljam [LA]ya sare shi. “Ina yi maku wasiyya da tsoron Allah,da fa]in gaskiya,da kuma yin aiki domin samun lada wajen Allah,ku taimaki wanda aka zalunta,da kuma nizamin[tsara] al’amuranku,da kuma gyara tsakaninku,ku kuma kyautata ma marayu kada ku tozartasu,da kuma kyautata ma ma}wabtanku,da kuma aiki da Al}ur’ani mai girma da kuma ri}o da Ahlu baytinsa,da kuma jihadi da dukiyoyinku da kuma rayukanku da kuma harsunanku fisabilillahi,na horeku da sadar da zumunci da kuma yin kyauta,ina yi maku kashedi da yenke ma juna,kada kuma ku bar umarni da ma’arufi da kuma hani da munkar,da kuma yin sallah cikin lokacinta,da kuma bada zakka,da kuma girmama ba}o,da kuma son miskinai da zama tare dasu,da kuma yin tawadi’u,da kuma tausayawa wa]anda suke cikin bala’i,da gajarta buri da kuma guje ma duniya,da dai sauran wasiyyoyi masu yawa da Imam Ali[AS] yayi ga mutane dabam dabam gab da zai bar duniya,alal misali a ranar }arshe ta rayuwarsa a wannan gida na duniya yake tambayar Hujur ]an Adiyy mi zaka ce idan wata rana tazo da za a bu}aci kayi min bara’a? Ya ce wallahi ya Amiril Muuminin da za a daddatsani da takobi gudunwa-gudunwa saannan a }ona ni da wuta ba zan ta~a yi maka bara’a ba.Shine Imam Ali ya ce masa ya Hujur ka yi gaskiya,Allah ya saka maka da alhairi.Haka abun ya faru bayan shekaru da shahadar Imam Ali[AS] wata rana sai Mu’awiya ya bu}aci Hujur da yayi bara’a ga Imam Ali,sai ya ce masa baka isa ba har abada ina tare da Imam Ali,shine Mu’awiya yasa aka kashe shi.A ‘yan shekarun nan magadansa a aiki suka tono }abarinsa,duk da bushewa da kuma }e}ashewar zukatansu abun ya basu mammaki domin da suka tono }abarin sai suka ganshi kamar ka ce yau ne aka sashi cikin }abarin.
Insha-Allah a darasi na gaba za a kawo hadisai suma a}alla guda 40 wa]anda aka ruwaito daga Imam Hassan[AS] haka-haka har mu kai ga na Imam Mahdi[AF] Insha-Allah. ~~

Daga wakilinmu ::AMMAR ABUBAKAR SHADOW
08055066884

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post