🇮🇪Ma'asumah Nigerian News Update
Tare da wakilinmu
MJ Matashi Ibrahim
#Sheikh Zakzaky (H)
To, kunga idan Allah Ta'ala ya gwada ka, abin da yakeso da kai shine kaci jarabawar, in kaci shi kenan an gama, sai lambar yabo. To, dole kuwa in za'a jarabta ka, dole a jarrabaka da abin dayake mai wahala. Kunsan ko jarabawar da akeyi a makarantu, ya jarabawar take? In aka rubuta jarabawar kowa yaci dari bisa dari, ya zama jarabawa? A'a.
Lokacin ina makaranta a kano, nidai bai koyar daniba, amma mutumin yana da dan tabin hankali ana ce masa Abdukadir, wani bamisire. Wai shi jarabawarsa, imma Mi'a bil Mi'a wa imma Sifir. Haka yake maki. Inya kallara idonsa, dama baya gani sosai, in yaga rubutunka yana da kyau sai yace Mi'a Faukal Mi'a. Kuma ko ka amsa daidai in ya ga rubutun gaja-gaja sai yace sifir. Shi makinsa kenan, kodai kaci dari bisa dari ko kaci sifili! Nibai koyar da ajinmuba, amma dai a shekarar da muke ya koyar da wasu, tunda muna da ajujuwa hudu ne a shekara guda ABCD, to ya koyar da yan C da B suna ta kuka. Wani ya iya amma kuma dai yayi rashin sa'a ran nan ziro ya samu, wani kuma yayi sa'a yasami dari, wani kuma bai iya komai ba yace shi gaskiya bai gane Arabiyya din nan ba. Sai yaje ya sami wani littafi ya haddace wani shafi, sai yazo ya rubuta shafin. Sai ya ce duk Mi'a.
To wannan ba jarabawa bace. Kyawun jarabawa (shine) ya zamana an tambaye ka wani abu ne wanda yake ko zaka iya ci ko za iya faduwa. In ya zama duk ci za kayi, to ba jarabawa bace. In ya zama duk gaduwa zakayi, shima ba jarabawa bace. "La yu kallifullahu nafsan illa wus'aha".
Sabo da haka duk lokacin da aka sa jarabawa da zaka iya ci. Kuma zai yiwu ka ci duk. To za a jarabtaka ne da abubuwa da daman gaske, "Wala Nabluwannakum bi Shai'in Minal Khaufi wal Ju'i wa Naksin Minal Amwali wal Amfusi Wasthamarat wa Basshiris-Saabireen". To kaga jarabawowin kenan. Tsoro, za a jarabtaka da tsoro. Kunga na farko akwai wadanda aka firgitar dasu. Akace masu, "Innannaasa kad Jama'ulakum Fakshshauhum". Sai suka ji tsoro? "Fazadahum Imanan wa Kalu Hasbunallahu wa Ni'imal Wakeel".
Su muminai ne akazo ana basu tsoro. Wani yace, "a'a kai! Zaku cimma runduna, ta shirya sosai, mayaka majiya karfi da muggan makamai. Wai yana so yaba su tsoro. Kai yadda na gan ku nan zasuyi loma daya ne da ku. Shi ya dauka muminai zasuji tsoro ne. Kawai sai yaga ana ta fara'a. Ana malam ya? Ashe yau kuma Alhamdulillahi zamuyi shahada, masha allahu! Wannan shine abin da Allah da Manzo sukayi mana alkawari. Kuma Allah da Manzon sunyi gaskiya.
Koda yake da Hausa ne. Ana cewa a cikin AlkuR'ani ba a fadin haka nan. Idan kace Allah da Manzonsa sai kace yayi gaskiya. "Wallahu wa Rusuluhu Ahakku Anyurduhu". Ba a cewa "Wasadakaa" ba. "Wallahu wa Rasuluhu Ahakku Anyurduhu", ba 'Yurdouhum' ba. Wato inka fadi Allah, ba ka gwama shi da kowa.
Masha allah zamu tsaya anan insha allah zamuci gaba inyana yi yabada in anga kuskure daga ni mai rubutune badaga jagoraba.
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky