@Ma'asumah Nigerian News Update@
Duk da a lokacin ba a haifeni ba, amma tarihi ya tabbatar da cewa Malama Zeenat Ibrahim (matar Sayyid Zakzaky(h) itace farkon sanya cikakken Hijabi a wannan kasa tamu Najeriya dama makota, tun bayan disashe daular Mujaddadi Shehu Dan Fodiyo da turawan mamaya suka aiwatar. Bana tsammanin akwai ma'abocin adalcin da zai musa wannan zancen. Idan kuwa ya tabbata haka, to lallai ya kamata wannan baiwar Allah da ta farfado da wannan ibada ta kasance a cikin littafin tarihi na musamman a wannan kasa tamu, musamman ga iyayen mu mata.
Hatta a fidira ta hankali (koda addini bai hukumta wannan ba) babu mai tunanin cewa kasancewar matan mu cikin tsaraici abu ne mai kyau, domin babbar kofa ce ta haifar da baraka da yaduwar fasadi a cikin al'umma. Bugu-da-kari, sai gashi tsarkakakken addini na Islama ya sake tabbatar da hakan. Abin takaici sai ya kasance mun wayi gari cikin halin ko-in-kula da al'amarin Hijabi ga matanmu. Wannan yayi sanadiyyar asarar tarbiyya da cikakkiyar kunya ga 'ya mace. Ya kake tsammani idan ace yau ga wani wanda yayi sanadin farkar da al'umma daga dogon barcin da suke akan wannan al'amari ?
Bisa al'ada, duniya takan sanya duk wani jarumi da yayi abin yabawa ko wani aikin Alkhairih a cikin kundin tarihi domin tunawa dashi da kuma wannan abin yabawa da ya aikata wanda al'umma ke amfanuwa dashi. Idan hakane, mai zai hana ba za'ayi amfani da wannan dama (ranar Hijabi ta duniya) domin tunawa da wacce ta farfado da wannan babbar sunnah ta Hijabi a wannan nahiya tamu ba? (Ina magana ne da iyayen mu mata musamman na wannan kasa Najeriya a k'alla).
Ni kam banga wata mace da tazo da Alkhairih ga al'umma fiye da Alkhairin da wannan baiwar Allah Malama Zeenat Ibrahim tazo dashi ba. Sabida haka ita ce mafi cancanta da girmamawa fiye da duk wata mace da ake girmamawa a wannan kasa tamu. Hijabi yana daga wajiban da Allah Ya wajabtawa matanmu, rashin kiyayesa kan iya jefa al'umma cikin halaka da hasara a duniya da lahira. A matsayinki ta mace; Wane tukwaici zaki baiwa wacce ta tono miki da wannan babbar sunnah bayan an bizne ?
Macen da tafi cancanta da girmamawa a sakamakon gudummawar da ta baiwa al'umma, amma sai gashi itace mafi abar zalumta a cikin mata a wannan zamanin. Ta yaya zaki taimaka mata don samuwar yancinta ? Wata kila hakan ya zama daga tukwaicin da zaki bata dangane da alkhairinta gareki.
- Abbakar Ibraheem Kudan.
01/01/2020