🇮🇪Ma'asumah Nigerian News Update
Tare dawakilinmu
MJ Matashi Ibrahim
Mu'utamar na bauci ayau jawabin:-
-Sheikh Adamu Tsoho Jos
A yanzu muna marhala na wakiya, kuma ya kamata mu fahimci Menene hadafin ita wannan Harka din. Wannan harka ba kana ma wani bane, ba kana wa Sayyid bane kana yiwa kanka ne. Malam ya Dora mu akan Ilimi da tarbiya shiyasa muka banbanta da sauran mutane.
Shi yasa tun farko Malam ya assasa Ta'alimomi da wasu abubuwa muhimmai a wannan harka. Kamar yadda yake Jagoranmu gida daya ne haka hadafin mu daya ne. Bangaren Matasa, Mata, da sauran dukkan bangarorin da ake da su mu sani cewa hadafin mu daya ne karshen al'amarin shine neman yardan Allah.
Shi yasa kullum abinda Malam suke so daga gare mu shine 'MU GYARA KAN MU', kuma gyara kai baya samuwa sai da ilimi da tarbiya. Ita Duniya nan Allah bai yi ta wajen zama ba ko Hutu haka ma rayuwa ba zata wanzu ba. In ka duba canji da marahil da kake bi tun kana cikin mahaifiyarka ka a haifeka kana jariri sannan har ka girma.
A da can in muna da'wa a tsaye muke ba gajiya haka kuma zaku kasance. Ya kamata 'yan uwa matasa su mai da hankalinsu yanzu hadafin wannan Gwamnatin shine rusa harka Islamiyya. A zamanin Obasanjo yaso ya rusa wannan da'awa tun daga lokacin muryan wannan da'awa take bunkasa, kuma suna gani zai zama babban barazana ga hukuman Nigeriya.
Dan haka run daga waccan lokacin duke ta kulle-kulle ya za'ayi a rusa wannan harka. Tun daga wakiyar John Madaki, Sani Abacha, to sai kuma ga wannan wakiya din wacce ta wuce waki'oin da aka yi. Wannan wakiya sun so kashe malam ne saboda suna tunanin cewa matukar ba kashe Malam aka yi ba ba zasu iya kashe wannan da'awan ba. Kuma yanzu babban hamkoron su shine su rusa matasa.
Lallai a wannan lokaci yana da matukar muhimmanci a nemi jawaban su Malam na baya da can dana yanzu. Wannan zai kara nuna ma cewa sauraron jawaban su Sayyid zai sa kai fahimci Menene kiran Malam (H). Kada ya zama kawai an takaita zuwa taron Mu'utamar ya zamo akwai wani lokaci da za'a ware na sauraren jawabuka. Yanzu harka tana bukatan ma'aikata ne wanda suka fahimci Menene hakikatan da'awar su Malam.
Don haka Ni'ima na wulaya baiwa ce babba, wanda duk wanda Allah ya mai Wannan baiwa din bai taimakawa Ahlul-bait ba to yaci amana na su Ahlul-bait ne. Taimakawa wannan da'awa shine zai zamo anci riban na fahimtar wulaya. A lokaci guda kuma ya kasance ya zamu taimaki junan mu, a lokacin da kake nema ku zama salihai to yi kokari ka taimakawa 'Dan'uwan ka.
Daga karshe Malam ya kawo wata kisa na Annabi Musa wanda ya karkare jawabin sa da ita.
Kadan daga wani yanki na jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos, wanda yayi yanzu haka wajen Taron Karawa Juna Sani a Garin Bauchi.
#Mu'utamarMatasaBauchi2020
Tags:
Jawaban Malamai