@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MARABA DA ZUWA YAA HASHEEM 'DAN HASHIMAAWAH
Imam Ali (A.S )mutum ne mai kyakkyawar nasaba ta bangaren Uwa da Uba, shine mai cikakken rana, wata da kuma,shekarar da aka haife shi daga cikin Sahabbai .
Shi kadai ne wanda za a iya kawo maka rana da watan da aka haife shi ba tare da wani kame-kame ba, ko menene dalilin hakan?
Idan kace saboda shi yaro ne, sai nace maka amma ai an san rana da watan da aka haifi fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S.A.W.W )wanda ya riga shi zuwa duniya.
An haife shi ne ranar juma'a, 13 ga Rajab, shekara ta 30 daga shekarar Giwa, 23 kafin Hijrar Ma'aiki. Wato lokacin Annabi (S.A.W.W )na da shekara 30 kenan a duniya.
NASABARSA (A.S )
(1)- TA WAJEN MAHAIFI:- Shine Aliyu Bn Abiy 'Dalib Bn Abdulmudallib Bn Hashim Bn Abdulmanaf Bn Qasaiyi Bn Kilab Bn Murrata Bn Ka'ab.....
(2)- TA WAJEN MAHAIFIYA:- Aliyu Ibn Fadimatu Bnt Asad Bn Hashim ...
Mahaifinsa da mahaifiyarsa sun hadu ne kan kakansa na biyu, wato Hashim.
Manzon Allah (S.A.W.W )na cewa:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ HAQIQA ALLAH (T )YA ZABI ISMA'IL DAGA CIKIN 'YA'YAN IBRAHIM, KUMA YA ZABI KINANATA DAGA DAGA 'YA'YAN ISMA'IL, KUMA YA ZABI QURAISHU DAGA CIKIN KINANATA, KUMA YA ZABI BANU HASHIM DAGA CIKIN QURAISHU , NI KUMA YA ZABENI DAGA BANU HASHIM. SABODA HAKA NI ZABABBE TSATSO NE MAFI GIRMAN ZABABBUN TSATSON LARABAWA .‘’
Kenan Imam Ali (A.S )cikakken Bahashime ne gaba-da-baya , sannan shine farkon Bahashime wanda ya fito tsakanin Hashimawa biyu .
MARABA DA ZUWA
YAA
HASHEEM
D
A
N
HASHIMAWA !!!
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-09039791509
~25th February, 2020.