Akhlaq: Kyautata kalamai ga iyali, kan janyo zaman lafiya!!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KOYARWAR IMAM ALI (A.S )

Sau da yawa matsalar da ake samu cikin gida ta fuskacin zamantakewa da iyali ana samu ne daga mazaje.

Mafi yawa daga mazaje su suke haifar da rashin zaman lafiya da iyali sakamakon rashin sanin haqqoqinsu da rashin iya zama dasu bisa halayensu.

Tare da cewa Allah (T )na cewa:

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUYI ZAMANTAKEWA DASU BISA SHARI'A (ta hanyar sauke haqqoqinsu da ke kanku ), IDAN KUMA KUKA QI SU (don ganin wasu abu da ba ku so daga gare su ), TO, AKWAI TSAMMANIN KU QI ABU, KUMA ALLAH YA SANYA ALBARKA MAI YAWA A CIKINSA .‘’

Kenan ana so mu kasance masu haquri dasu ko don wani abu daga gare su na so wanda ba a rasawa tare da su.

A wani guri kuma Imam Ali (A.S )na cewa:

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KU SULHUNTA DASU A KOWANNE IRIN HALI, KUMA KU RIQA KYAUTATA MAGANA DASU TA HANYAR DADADAN KALMOMI (ina sonki, uwar sanyin idanuwanmu kenan, kallon fuskarki na sanyaya min zuciya , babu wanda zai sami irin ki sannan yayi sha'awar wata mata d.s ), AKWAI YIWUWAR SU CANZA WANNAN AIKI (wanda ba ka so )ZUWA MAI KYAU (irin wanda kake so ).‘’

(BIHARUL-ANWAR, J:103, SH:223)

Amma maimakon yin haka sai kaga wasu mazajen basu iya dadadan kalamai ga matansu don nishadantar dasu ba in ba lokacin neman aurensu ba.

Idan kana son ganin fara'arsu to, ka same su wajen matar,waje wacce ake aqilon ganin ta shigo gida a matsayin matarsa.

Daga wakilanmu na  Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

07059911360-09039791509

~25th February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post